A yau Litinin ne Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin tana damuwa sosai kan yadda rikici ya ke kara kamari a kasar Afghanistan.
Mista Geng ya fadi haka ne yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing. A ranar 21 ga wata da yamma ne, aka kaiwa hari wani sansanin soja na rundunar tsaron Afghanistan dake a lardin Balkh na kasar, inda mutane a kalla 140 suka rasa rayukansu ya zuwa yanzu. 'Yan tawayen Taliban sun yi shelar daukar alhakin kai harin. Yayin da mista Geng ya amsa tambayar da ke shafar lamarin, ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi kira ga sassa daban daban na Afghanistan da su hau teburin sulhuntawa karkashin jagorancin al'ummar Afghanistan, a kokarin kiyaye zaman lafiya da ci gaban kasar ta Afghanistan. (Tasallah Yuan)