A cewar ministan na kasar Sin, yadda aka kirkiro dandalin "tsoffin kasashe masu al'adu" a kasar Girka yana da ma'ana sosai, bisa la'akarin da yanayin rashin tabbas da ake fuskantar a duniyarmu. Ta wannan hanya, a ganin ministan, za a samu gano wasu dabarun da aka taba aiwatarwa a tarihin dan Adam, wadanda za su taimakawa kokarin daidaita matsalolin da ake fuskanta a yanzu.
Wang Yi ya kara da cewa, kasar Sin ta gabatar da shirin "ziri daya da hanya daya" ne domin neman yayata akidar "hanyar siliki", wadda ta shafi kiyaye zaman lafiya da hadin gwiwa, da bude kofa, da hakuri, da koyon fasahar juna, da amfanar juna.(Bello Wang)