in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
(Wakilinmu Ahmad Fagam a lardin Shanxi)Kamfanin fina finai na Qujiang yana ba da gudummawa kan mu'amalar al'adu a tsakanin kasa da kasa
2017-04-24 10:20:23 cri

A ranar farko ta wannan ziyarar aiki wanda gidan radion kasar wato China Radio International CRI ya shirya, a yau Lahadi 23 ga watan 3 shekarar 2017, mun ziyarci wani kamfanin shirya fina finai wato Qujian Film & TV Industry dake birnin Xi'an.

Shugabar gudanarwar wannnan kamfani ta gudanar da muhimmin jawabi game da tarihin wannan kamfanin, inda ta bayyana mana cewa, an kafa wannan kamfani ne a shekarar 2006, wato shekaru kusan 11 da suka gabata.

Kamfanin yana gudanar da ayyuka da dama, da suka hada da shirya fina finai, da shirye shiryen fim na gidan talabijin , da kuma shirya bayanan tarihin kasar sin da al'adun alummar sinawa.

Wani muhimmini batu data bayyana shine, wannan kamfani yana yin hadin gwiwa da gwamnatin kasar Sin wajen shirya fina finai da suka shafi tarihi da kuma al'adun kasar Sin, kana gwamnatin Sin tana bada taimako da cikakken goyon baya ga wannan kamfani.

Daga lokacin da aka kafa kamfanin zuwa yanzu, , ya samu nasarori masu yawa wajen shirya fina finai sama da 30, da shirye shiryen fim na talabijin 33, da tarihin Sin da ala'dun sinawa 15.

Wani muhimmnin batu shine, wannan kamfani ya shirya fina finai game da tarihin kasar Sin da al'adun sinawa sama da guda 20, wadan da aka nuna a kasashen duniya sama 40 cikin harsunan wadan can kasashen, daga cikin wadan nan kasashen akwai Uganda, Rwanda da kuma Tanzaniya daga nahiyar Afrika.

A shekarar 2016, kamfanin Qujian Film & TV, ya shirya wani kasaitaccen biki game da shirin nan na ziri daya da hanya daya, wanda ya samu halartar alummomi daga yankunan daban daban da kasashen duniya sama da 50, gwamnatin Sin ta nuna matukar gamsuwa da yabo kan wannan biki da aka gudanar.

Ya zuwa yanzu kamfaninn Qujian Film & TV, ya samu kyautukkuka daga yankuna da kasashen duniya masu yawan gaske.

A nan gaba, kamfanin zai shirya wasu finai finai da suka shafi shirin nan na raya huldar kasuwanci da mu'amalar Sin da kasashen duniya wato shirin"ziri daya da hanya daya". (Ahmad Inuwa Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China