in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Kenya sun hallaka dakaru 52 na kungiyar Al-Shabaab
2017-04-23 13:09:24 cri
Kafofin watsa labaran kasar Kenya sun ruwaito cewa, sojojin kasar dake karkashin tawagar wanzar da zaman lafiya da kungiyar tarayyar Afirka ta tura zuwa kasar Somaliya, sun hallaka 'ya'yan kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta Al-Shabaab da dama a kudancin kasar Somaliya.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin Kenya Kanar Joseph Owuoth ya fitar, ta ce sojojin kasar sun gano wata matattarar kungiyar Al-Shabaab a jihar Lower Jubba dake kudancin Somaliya, inda suka kai musu farmaki a ranar 21 ga wata, al'amarin da ya yi sanadin halaka yayan kungiyar 52, tare kuma da kwace makamai da harsasai masu tarin yawa.

Kanar Owuoth ya ce, ba za a dakatar da fatattakar mayakan kungiyar Al-Shabaab ba, har sai an murkushe kafataninsu.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China