in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana a nahiyar Afrika sun bukaci a kara zage damtse wajen kare dazuka
2017-04-23 12:38:33 cri
Masana a nahiyar Afrika sun bayyana samar da shirye-shiryen farfado da dazuka a matsayin matakan da suka wajaba, wajen inganta samun tsirrai a yankin kudu da hamadar sahara.

Masanan wadanda suka yi taro a Nairobi babban birnin kasar Kenya a ranar Juma'a, sun jadadda bukatar kare lalacewar dazuka ta hanyar samar da muhimman dabaru da dokoki da ware kudade domin samar da ci gaba mai dorewa a nahiyar Afrika.

Da yake jawabi, sakataren zartarwa na kungiyar dake fafutukar kare dazuka dake Nairobi wato Africa Forest Forum, Godwin Kowero ya ce samar da ingantaccen muhallin rayuwar hallitu, zai karfafa kyakkyawar makomar nahiyar da kwanciyar hankali da kuma zaman lafiya.

Ya bayyana cewa, sauyin yanayi, da matsalolin shugabanci da karuwar adadin al'umma da kaura, na daga cikin kalubalen da dazukan Afrika ke fuskanta.

Har ila yau, Godwin Kowero ya ce idan har ana son farfado da dazuka daga lalacewa, jazaman ne Gwamnatocin kasashen Afrika su yi wa tsoffin dabaru gyaran fuska da karfafa amfani da dokoki da kuma shigar da al'ummomin cikin shirin.

Ya kuma bayyana rashin jin dadi game da yadda rashin amfani da dokoki da rashin kwararrun jami'ai ke tarnaki ga kare dazuka a kasashen Afrika da dama.

A nasa bangare, babban jami'in a sashen kare filaye da dazuka na hukumar kula da ayyukan Tarayyar Afrika Almami Dampa, ya ce kula da albarkatun dake dazuka yadda ya kamata ita ce muhimmiyar hanyar samun wadataccen abinci da ruwa da kuma makamashi a nahiyar mafi girma na biyu a duniya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China