in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala taron kwamitin ministocin harkokin waje na kungiyar SCO
2017-04-22 14:00:41 cri
A jiya Jumma'a ne aka kammala taron kwamitin ministocin harkokin wajen kungiyar kawance ta Shanghai a birnin Astana na kasar Kazakhstan, wanda aka fara a ranar 20 ga wannan wata.

A yayin taron, ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar, sun cimma matsaya daya, kan ci gaba da karfafa hadin gwiwa tsakanin mambobin kungiyar, wajen fuskantar kalubalen da suka shafi tabbatar da tsaron kasa da kasa, musamman ma a fannonin yaki da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi da masu aikata laifuffuka a tsakanin kasa da kasa da kuma jigilar miyagun kwayoyi.

Haka zalika, ana sa ran inganta hadin gwiwar mambobin kungiyar wajen kare tsaron bayanai da kuma fuskantar harkokin dake bukatar agajin gaggawa da dai sauransu.

Bugu da kari, ministocin sun nuna goyon bayansu ga kasar Sin game da gudanar da taron kolin tattaunawa kan hadin gwiwar kasa da kasa bisa shirin 'ziri daya da hanya daya' a ranakun 14 da 15 na watan Mayu mai zuwa a nan Beijing, babban birnin kasar Sin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China