in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta cimma nasarar harba kumbon dakon kaya na Tianzhou-1
2017-04-21 13:17:56 cri

A daren jiya Alhamis da karfe 7 da minti 41, aka yi nasarar harba kumbon Tianzhou-1 wanda ya kasance kumbon dankon kaya na farko na kasar Sin, kuma ya shiga falakinsa cikin nasara. Wannan shi ne kumbo mafi girma a yanzu haka a nan kasar Sin, ayyukan da kunbon Tianzhou-1 zai gudanar sun shafi jerin fasahohi, hakan zai aza harsashi mai kyau ga raya tashar sararin samaniyan kasar Sin. 

A daren ranar 20 ga wata da karfe 7 da minti 41, tare da babban ruri rokar daukon kaya samfurin Changzheng-7 ta tashi tare da kumbon Tianzhou-1 zuwa sararin samaniya.
Bayan kimanin minti sama da 20, shugaban sashen ba da umurni na yankin harba kumbon Tianzhou-1 mista Zhang Xueyu ya sanar da cewa, an samu cikakkiyar nasarar harba kumbon dankon kaya na Tianzhou-1. 

"Cibiyar kula da zirga-zirgar sararin samaniya ta Beijing ta bayyana cewa, rokan daukar kayan na Changzheng-7 na tafiya yadda ya kamata, kumbon dankon kaya na Tianzhou-1 ya shiga falakinsa kamar da aka tsara, farentan dake adana makamashin mai amfani da hasken rana na shimfida yadda ya kamata. An harba kumbon Tianzhou-1 cikin nasara!"
Sinawa da yawa suna kira kumbon Tianzhou-1 "Mai dakon kaya zuwa sararin samaniya", saboda kumbon shi ne zai rika daukar nauyin kai kayayyaki tashar sararin samaniya da ake fatan ginawa a nan gaba. A matsayinsa na kumbon dakon kaya na farko na kasar Sin, kumbon Tianzhou-1 na hade da sashen kaya da sashen dake harba na'urori zuwa sama, nauyin sa a yayin tashi ya kai kimanin ton 13, nauyin kayan da zai iya dauka ya kai ton 6.5. Mataimakin babban mai tsara tsarin kumbon mista Xu Xiaoping ya bayyana cewa, a matsayin sa na wani muhimmin sashe mai matakai guda uku na aikin da ya shafi kumbon da ke daukar 'yan sama jannati, wannan aikin harba kumbon na farko na da ma'ana kwarai:

"Kumbon dakon kaya dake tashi sama mafi girma na kasar Sin, wanda ke daukar na'urori da gwaje-gwajen fitowar 'yan sama jannati daga akwati, ta yadda ya aza harsashi ga amfanin tashar sararin samaniya a nan gaba."
Idan aka kwatanta shi da sauran ayyukan jigilar 'yan sama jannati, aikin kumbon Tianzhou-1 na da halin musamman nasa. Mista Zhang Xueyu ya bayyana cewa, 

"Akwai bukatar kumbon Tianzhou-1 ya shiga falakinsa daidai kwarai, hakan shi ke tabbatar tsarin yankin harba kumbon. Wannan shi ne karo na farko da aka zabin hanyar harba kumbon kai tsaye a maimakon tsara wani tsawon lokaci, dole ne a harba roka a lokacin da aka tsara, bai kamata a tsawaita ko canja lokacin ko kadan."
Babban aikin Tianzhou-1 a wannan karo, shi ne kai kaya ga kumbon Tiangong-2, inda zai hade da dakin gwajin kumbon dake sararin samaniya da kara farfelansa a kan hanyar dake falakinsa, inda za a sarrafa wasu muhimman fasahohi, ta yadda za a jarraba sabon tsarin gwaji na kasa. Mai ba da taimako ga babban injiniya na cibiyar kula da zirga-zirgar sararin samaniya na kasar Sin mista Cui Xiaofeng ya bayyana cewa, akwai bambanci tsakanin ayyukan yin awo da sarrafawa na Tianzhou-1 da na sauran ayyuka na gaba.

"Da farko, kumbon ya dara sauran kumbunan baya, wannan ya sa aka kara bukatu a fannin aikin fassara. Na biyu, za a yi gwaje-gwaje da ba a taba yin irinsu a baya ba, ciki har da kara karin farfelan dake kara saurin shigar kumbon cikin falakinsa, wannan yana cikin sharadin da aka wajabta da za a samar a tashar sararin samaniya cikin dogon lokaci. Na uku, a yayin wannan gwaji, za a tabbatar da hadewar kumbon Tianzhou-1 da na Tiangong-2 cikin saurin, bayan an sarrafa wannan fasaha, za a rage lokacin da 'yan sama jannati ke dauka wajen shiga tashar sararin samaniya."

Bayanai na nuna cewa, bayan da aka harba kumbon Tianzhou-1, zai kama hanyar shiga falakinsa mai nisan kilomita kimanin 380, daga baya kuma zai hade da tashar binciken sararin samaniya na Tiangong-2 dake kan hanyar kewaya sararain samaniya har sau uku, inda za a gudanar da aikin kara karfin farfelarsa har sau uku, kana kumbon zai yi zirga-zirga a kalla na tsawon watanni 3.

Bisa shirin da ya shafi kumbon da ke daukar 'yan sama jannati na matakai uku, aikin Tianzhou-1 shi ne na karshe a tashar gwajin sararin samaniya, kuma shi ne muhimmin aikin gina tashar sararin samaniya. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China