in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar wakilai ta kasar Birtaniya ta amince da gudanar da babban zabe kafin lokacin da aka tsara
2017-04-20 13:14:04 cri

Majalisar wakilan kasar Birtaniya,ta kada kuri'a kan batun gudanar da babban zabe kafin lokacin da aka tsara, wanda firaminista Theresa May ta gabatar, inda kuma aka amince da shi da kuri'u masu rinjaye.

Wannan na nuni da cewa, za a kaddamar da babban zabe a ranar 8 ga watan Yunin bana a kasar Birtaniya.

Fadar firaministar kasar ta bayyana cewa, babban zaben ba zai yi tasiri ga jadawalin ficewar kasar daga kungiyar tarayyar Turai ba.

A ranar Talata 18 ga wata ne, firaministar kasar Birtaniya Theresa May ta sanar da gudanar da babban zabe kafin lokacin da aka tsara bisa hujjar kiyaye babbar moriyar kasarta, lamarin da ya wuce tsammanin mutane, har ma a jiya, Jaridar Daily Telegraph ta kasar ta sifanta kudurin a matsayin na ba zata.

A jiyan ne kuma, majalisar wakilan kasar ta kada kuri'a kan kudurin, inda aka zartas da shi bisa rinjayen kuri'u, wato an samu kuri'u da suka amince da shi har 522, yayin da aka samu masu adawa guda 13 kawai.

Sakamakon kuri'ar da aka kada, ya sheda cewa, bayan babban zabe da aka yi cikin watan Mayun shekarar 2015 da kuma kuri'a da aka kada kan janye jiki daga kungiyar EU a watan Yunin bara, masu zabe a duk fadin Birtaniya za su sake jefa kuri'a, da ma an yi shirin gudanar da babban zaben a shekarar 2020.

An yi hasashen cewa, dalilin da ya sa Theresa May ta tsai da wannan kuduri shi ne, son kiyaye fifikon Jam'iyyar Kwanzabatib ta Birtaniya a majalisar wakilan kasar, ta yadda sabuwar gwamnatin kasar za ta iya wakiltar kasar wajen tattaunawa tare da kungiyar EU kan batun ficewar kasar daga kungiyar. Haka kuma a cikin muhawarar da aka yi cikin majalisar kafin jefa kuri'ar, Theresa May ta jaddada cewa, ta tsai da kudurin shirya babban zabe kafin lokacin da aka tsara ne bisa la'akari da muradun kasar. tana mai cewa,

"Game da halin rarrabuwar kai da ake samu a cikin majalisarmu, na riga na yi bayani sarai, kullum wasu mutane kan zarge mu bisa wannan hujja, domin raunana karfinmu na tattaunawa tare da EU. Amma za mu yi kokari don hana abkuwar hakan. na yi imanin cewa, abin da ya fi muhimmanci yanzu shi ne, inganta hadin gwiwa cikin majalisarmu, a maimakon kawo baraka. Don haka, kada kuri'a don goyon bayan shirin gudanar da babban zabe kafin lokacin da aka tsara, kyakkyawan kuduri ne. Sannan, ya kamata mu girmama tare da amincewa da sakamakon babban zaben, ta yadda sabuwar gwamnatin za ta iya yin iyakacin kokarinta don kiyaye muradun Birtaniya a cikin tattaunawar da za ta yi da EU kan janyewa daga kungiyar."

A nasa bangaren kuma, Shugaban Jam'iyyar Leba ta kasar Jeremy Corbyn ya yi maraba da wannan kudurin, inda yake ganin cewa, gudanar da babban zabe kafin lokacin da aka tsara zai ba 'yan kasar wata damar ta zabar jam'iyyarsa. Amma a waje daya kuma, ya soki Theresa May, ya na cewa, ta ci amanar jama'a.

"Muna maraba da shirin gudanar da babban zabe kafin lokacin da aka tsara, sabo da wannan zai ba 'yan kasarmu wata damar zabar Jam'iyyar Leba. Ko da yaushe gwamnatin Jam'iyyarmu na sanya muradun jama'a gaban komai. Firaministarmu ta ce, ta tsai da wannan kuduri ne cikin dan lokaci saboda ba ta da wani zabi na daban. Amma makwanni hudu da suka gabata, kakakinta ya taba nanata cewa, ba za a shirya babban zabe kafin lokacin da aka tsara ba. Ganin yadda Firaministar ta saba alkawarin da ta dauka, yaya jama'armu za su sake amincewa da maganganun da za ta fada? Ban da wannan kuma Firaministar ta ce, za a farfado da tattalin arzikin kasarmu, amma galibin 'yan Birtaniya sun fi shan wahalar rayuwa idan aka kwatanta da shekaru 7 ga suka gabata, duk da cewa a lokacin ma, ana karkashin jagorancin Jam'iyyar Kwanzabatib. Don haka, shirin gudanar da babban zabe kafin lokacin da aka tsara, zai ba jama'ar kasar wata damar canja zabinsu na da."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China