in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya yi kira da a daidaita batun Libya ta hanyar siyasa
2017-04-20 10:39:38 cri
Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake Majalisar Dinkin Duniya, Mista Wu Haitao, ya bayyana a jiya Laraba cewa, ya kamata a nace ga bin hanyar siyasa domin daidaita batun kasar Libya. Jama'ar Libya su ne za su jagoranci aikin shimfida zaman lafiya a kasar.

A wajen taron da kwamitin sulhun MDD ya shirya dangane da batun Libya, Mista Wu ya ce, an shekara guda da rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta Libya, amma aiwatar da shi bai samu nasara yadda ya kamata ba, har ma aikin shimfida zaman lafiya a kasar na fuskantar babban kalubale.

Wu Haitao ya ce, ya kamata bangarori masu ruwa da tsaki su gaggauta yin shawarwari, da kawar da duk wani bambancin ra'ayi tsakaninsu, a kokarin lalubo bakin zaren daidaita matsalolin kasar, da samun sulhu tsakanin al'ummar kasar.

Wu ya kuma ce, ya zama dole bangarori daban-daban a Libya su nuna juriya da hakuri, domin kaucewa daukar matakan soja.

Har wa yau, Wu ya yi kira ga kasa da kasa da su samar da tallafi ga kasar Libya, ya ce ya kamata MDD ta taka rawarta, haka kuma tawagar musamman da MDD ta tura zuwa Libya za ta gudanar da aikinta bisa ka'idojin kwamitin sulhun MDD. Bugu da kari, kawancen kasashen Larabawa da kungiyar tarayyar Afirka gami da kasashen dake makwabtaka da Libya, dole ne su himmatu wajen farfado da shawarwarin wanzar da zaman lafiya a Libya, da sulhunta bangarori daban-daban a Libya. Kasashen duniya ma dole su rubanya kokarin tallafawa Libya, tare da mutunta ikon mallakar kasa da 'yancin kan kasar.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China