in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta harba kunbon Tianzhou-1 nan da 'yan kwanaki
2017-04-19 20:40:17 cri
Cibiyar harba kumbuna ta kasar Sin dake Wenchang a lardin Hainan dake kudancin kasar Sin, ta ce ta kammala dukkanin gwaje gwaje da suka wajaba, gabanin harba kumbon dakon kaya na Tianzhou-1.

Cibiyar ta ce ta kallama gwajin harba tauraron ne a jiya Talata, ciki hadda ayyukan tsara rokar harba kumbon, da shi kan sa lafiyar kumbon. Sauran sun hada da wurin da za a harba shi, da ma sashen sarrafawa, da na sadarwa.

Hakan dai na nufin komai ya kammala, kuma tsakanin ranekun 20 zuwa 24 na watan nan na Afirilu za a harba kumbon.

Kumbon dakon kayan dai shi ne irin sa na farko wanda kasar Sin ta gina bisa fasahar ta, ana kuma sa ran bayan harba shi zai hade da dakin gwaji na Tiangong-2 dake can sararin samaniya, ya kuma samu karin makamashi yayin da yake kan falakin sa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China