Rahotanni na cewa wannan dakin karatu da aka fara ginawa a kan titin zuwa makarantar firamare ta Chengdu, na da fadin kusan sakwaya mita 1000, ana kuma fatan bude shi cikin shekara mai zuwa.
Kaza lika dakin na karatu zai kunshi dubun dubatar littattafai, da bayanai na sauti da na bidiyo, game da wannan dabba ta Panda, wadanda za a tsara cikin harsuna da dama. (Saminu Hassan)