in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
GDP na Sin ya karu da kaso 6.9 bisa dari a rubu'in farkon bana
2017-04-18 11:10:33 cri

Jiya Litinin hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar da alkaluma cewa, a rubu'in farko na bana, adadin GDP wato yawan kudin da aka samu daga sarrafa dukiyar kasa ya karu da kaso 6.9 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, kana tun daga watan Yunin bara, tattalin arzikin kasar ta Sin ya samu ci gaba yadda ya kamata har ya fi hasashen da aka yi.  

Alkaluman da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar jiya sun nuna cewa, a rubu'in farko na bana, adadin GDP na kasar Sin ya karu da kaso 6.9 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, adadin da ya karu da kaso 0.2 bisa dari idan aka kwatanta da karuwar da aka samu a rubu'in farko tsakanin shekarar 2015 da ta 2016, musamman ma adadin GDP a fannin masana'antu ya fi yawa har ya kai kaso 6.8 bisa dari, hakan zai sa kaimi kan ci gaban tattalin arziki a kasar.

Kakakin watsa labarai na hukumar kididdigar kasar Sin Mao Shengyong ya bayyana cewa, a rubu'in farkon bana, tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba yadda ya kamata har ya fi hasashen da aka yi. Yana mai cewa, "A takaice dai, tattalin arzikin kasar Sin ya samu yalwatuwa lami lafiya a rubu'in farkon bana, kuma ana ci gaba da gudanar da kwaskwarima kan tsarin tattalin arzikin, kana an samu ci gaba a bayyane a fannin kirkire kirkire, ban da haka kuma, zaman rayuwar al'ummar kasar yana kara kyautatuwa a kai a kai. Amma a halin da ake ciki yanzu, yanayin da kasashen duniya ke ciki da tsarin tattalin arzikin kasar Sin ba su da inganci sosai , a saboda haka ya kamata a kara sanya kokari domin cimma burin samun ci gaban tattalin arziki a kasar ta Sin."

Daga tsarin sana'o'in kasar, ana iya gano cewa, a rubu'in farkon bana, masana'antun kasar sun fi samun bunkasuwa, har adadin karuwarsu ya kai kaso 36.1 bisa dari dake cikin kwatankwacin adadin karuwar GDP na Sin, musamman ma tsakanin watan Janairu da na Fabrairun bana, adadin ribar da kamfanonin masana'antun kasar suka samu ya karu da kaso 31.5 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, ana iya cewa, karuwar masana'antu a Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da karuwar tattalin arziki a kasar.

Daga fannoni uku mafiya muhimmanci wajen raya tattalin arziki wato zuba jari da sayayya da fitar da kayayyaki zuwa ketare kuwa, a rubu'in farkon bana, sayayya ta fi taka rawa yayin da ake kokarin tabbatar da karuwar tattalin arziki har ya kai kaso 77.2 bisa dari. Game da dalilin aukuwar lamarin, Mao Shengyong yana mai cewa, "A rubu'in farko na bana, kudin shiga na al'ummar kasar Sin ya karu da kaso 7 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, shi ya sa al'ummar kasar suna kara kashe kudin da suka samu domin kyautata zaman rayuwarsu."

Bisa alkaluman da aka samu, an ce, a rubu'in farkon bana, adadin kudin da aka zuba kan aikin gina gidajen kwana a fadin kasar Sin ya kai RMB yuan biliyan 1929.2, adadin da ya karu da kaso 9.1 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara. Yanzu gwamnatin kasar Sin tana kokarin kyautata aikin samar da gidajen kwana, a karkashin irin wannan yanayi, ko gwamnatin za ta fitar da sabuwar manufa, Mao Shengyong ya bayyana cewa, "Nan gaba, ko za a kara zuba jari kan aikin samar da gidajen kwana a kasar Sin ko a'a, ana iya gano lamarin ta mahanga biyu, na farko, adadin gidajen kwanan da aka sayar da su a fadin kasar ya karu bisa babban mataki a shekarar bara, kawo yanzu, adadin ya ragu, kila hakan zai hana wasu su kara zuba jari kan aiki, na biyu kuwa, a wasu biranen kasar, an kara samar da filayen gina gidajen kwana, kila ne hakan zai sa kaimi ga 'yan kasuwa su kara zuba jari kan aiki, saboda ya dace a zuba ido don ganin abinda zai faru a nan gaba."

A sa'i daya kuma, Mao Shengyong ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta fara daukar sabbin matakan sarrafa aikin samar da gidajen kwana ne a ranar 17 ga watan Maris na bana, ko shakka babu matakan za su kawo tasiri ga tattalin arzikin kasar da farashin gidajen kwana a kasar da sauran fannonin dake da nasaba da aikin samar da gidajen kwana, amma ba yanzu ba sai bayan karshen wannan wata ke nan.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China