in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Huang Dafa na yaki da talauci
2017-04-18 14:17:21 cri

Huang Dafa: a matsayin wani 'dan jam'iyyar kwaminis, kamata ya yi na gudanar da hakikanan ayyuka ga fararen hula.

Domin warware matsalar karancin ruwan sha, da shayar da gonaki da kauyensu ke fuskanta, a cikin tsawon shekaru 36, wato tun daga shekaru 60 na karnin da ya wuce, tsohon sakataren kauyen Tuanjie na garin Pingzheng dake yankin Bozhou na birnin Zunyi mista Huang Dafa, ya jagoranci mazauna kauyen wajen gina wata magudanar ruwa a hayin babban dutse arewacin lardin Guizhou, wadda tsawon muhimmin sashenta ya kai mita dubu 7.2, kuma reshenta ya kai mita dubu 2.2.

Mazauna wurin sun kira ta da suna "Magudanar Dafa". Game da yabo da mazauna suka nuna masa, Huang Dafa ya ce, "ni manomi ne dake karkara mai nisa, na yi wannan aiki ne domin fararen hula, wannan ba wata alfarma ba ce. Sai dai a cewar sa muddin ba a manta da imanin farko da ake da shi ba, to za a iya samu ci gaba."

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China