in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta zabi lokacin da ya dace a tsakanin ranakun 20 da 24 ga wata domin harba kumbon daukar kaya mai lamba 1 na Tianzhou
2017-04-17 13:37:23 cri

Rahotanni daga ofishin kula da ayyukan nazarin kumbon daukar mutane na kasar Sin, na cewa an riga an kammala aikin hadawa, da kuma gwada fasahohin kumbon daukar kaya na Tianzhou mai lamba 1, da roka mai lamba 7 sufurin daukar kaya ta Changzheng, wanda ake sarrafawa daga nesa a yau Litinin, a filin da za a harba su.

Wani jami'i wanda ke kular da aikin ya ce, za a yi aikin bincike da kuma gwajin sassa daban daban na kumbon daukar kaya na Tiangong, da rokar baki diya. Bayan an tabbatar da yanayin karshe da suke ciki, za a dura masu makamashin harbawa.

Bisa shirin da aka tsara, za a zabi wani lokaci mafi dacewa a tsakanin ranakun 20 da 24 ga wata domin harba su. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China