Mahalarta jarrabawar sun zo ne daga yankunan kasar Sin, wasu kuma sun zo daga kasashen Rasha, Amurka da kuma Brazil da dai sauran kasashe da yankuna na duniya.
Tsawon lokacin jarabawa ya kai mintoci 210, inda aka yi jarrabawar kan fannonin binciken halin dan Adam, harsunan waje da kuma ilmin musamman dake shafar wasannin Olympic da sauransu.
Haka kuma, a wannan rana, kwamitin ya shirya wata jarabawa ta musamman, inda ya zabi mutane 76 da suka yi jarrabawar, domin nema ma'aikatan da za su dace wajen kula da ayyukan shirya wasannin Olympics na lokacin hunturu. Kuma, ma'aikatan da kwamitin yake neman a halin yanzu, ya kamata su taba yin irin wannan aiki a baya, kamar wanda ya taba shirya babbar gasa ta kasa da kasa, sannan kuma yake da kwarewa kan harsunan kasashen waje. (Maryam)