in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman Sin: ya kamata a warware batun Gabas ta tsakiya a dukkan fannoni
2017-04-15 13:34:59 cri
Manzon musamman na kasar Sin kan batun Gabas ta tsakiya, Gong Xiaosheng, wanda a yanzu haka ke ziyara a kasar Masar ya ce, kasar Sin na son yin kokari tare da hadin kan kasashen da batun ya shafa, wajen warware muhimman batutuwan dake ciwa Gabas ta tsakiya tuwo a kwarya, a dukkan fannoni.

Gong Xiaosheng ya bayyana haka ne a jiya Juma'a, yayin da yake ganawa da manema labrai na kasar Sin a birnin Alkahira.

Ya kara da cewa, warware matsalar a dukkan fannoni na hade da wasu abubuwa, yana mai cewa, bai kamata kasashen duniya su zabi wasu batutuwa su ba muhimmaci su kyale wasu ba.

Jami'in ya ce bai kamata a kyale batun Palestinu ba, domin ya kasance muhimmin batu a yankin Gabas ta tsakiya.

Har ila yau, ya ce yayin da ake kokarin inganta zaman lafiya, kamata ya yi a yi la'akari da yadda za a raya kasa bayan yaki da bunkasa tattalin arziki da zaman takewar al'umma da sauran abubuwa.

Baya ga haka, Gong ya ce, babu abun da kasar Sin za ta mora daga rikicin yankin Gabas ta tsakiya, ya na mai cewa, jefa yankin cikin rikici bai dace da moriyar kasashensa ba, kuma Kasar Sin na fatan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban tattalin arziki a kasashen dake yankin. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China