Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya yi gargadin cewa, barkewar yaki a zirin Koriya, ba zai haifarwa kowa da mai ido ba. Mr. Wang yayi fatan daukacin kasashen duniya za su kai zuciya nesa domin kaucewa kara dagula al'amura.
Ministan wanda ya yi wannan tsokaci yayin zantawar sa da 'yan jaridu a Juma'ar nan bayan ya gana da takwaransa na Faransa Jean-Marc Ayrault, ya ce dangantaka na kara tsami tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa. Kuma wannan yanayi ya dace da ja hankalin kowa.
Mr. Wang ya ce tun tuni Sin ke adawa da duk wani mataki na tada zaune tsaye, wanda ka iya rura wutar rikici. Kuma a bayyane take cewa, bisa tarihi warware takaddama ta hanyar shawarwari ita ce hanya mafi dacewa, a duk lokacin da aka samu rashin fahimtar juna.(Saminu Alhassan)