in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ko halin da Syria ke ciki zai kara rincabewa ko a'a?
2017-04-11 14:35:06 cri

A yanzu haka halin da kasar Syria ke ciki na dab da kara rincabewa, musamman ma game da batun yin amfani da makamai masu guba wajen harin da aka kaddamar a lardin Idleb na kasar a ranar 4 ga wannan wata. Kwanaki 3 bayan faruwar lamarin, sai kasar Amurka ta kaddamar da hari kan Syria, inda jiragen ruwan soja guda biyu na Amurka dake tsaya a gabashin Bahar Rum suka harba makamai masu linzami 59 kan sansanin sojan sama na Shayrat na lardin Homs. Bangaren sojan Amurka ta bayyana cewa, jirgin sojan Syria da ya kai harin ya tashi ne daga wannan sansanin.

Game da harin da aka kaddamar ta yin amfani da makamai masu guba, da lamuran da suka faru bayan lamarin, akwai wasu fannonin da ya kamata a dora muhimmanci kansu:

Da farko, a kasar Syria dama yankin Gabas ta Tsakiya bakin daya, masu tayar da jijiyar wuya kan lamarin kai hari ta hanyar amfani da makamai masu guba suna iya amfani da kowace irin hanya domin cimma burinsu. Sabo da haka, akwai yiwuwar za su ci gaba da amfani da makamai masu guba a rikice-rikicen dake kasancewa a tsakanin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya.

Na biyu, ana samun sabani tare kuma da neman moriya a tsakanin wasu manyan kasashen dake da alaka da batun Gabas ta Tsakiya, ciki har da Amurka da Rasha da dai sauransu, har ma a tsakanin kasashe daban daban dake yankin, har suna tuhumar juna, kuma suna nuna rashin amincewa da juna, saboda haka, ko wane lamarin zai iya kara tsanani har ya tayar da wani yaki a yankin, har ma rikici a tsakanin manyan kasashe. Don haka, wasu rukunoni dake boye suna kokarin amfani da damar don tayar da rikici, da karfafa tuhuma, da nufin karfafa tabarbarewar halin da ake ciki a yankin.

Na uku, bayan Donald Trump ya dare kujerar shugabancin kasar Amurka, har zuwa yanzu bai tabbatar da manufar da kasarsa za ta bi kan batun Gabas ta Tsakiya ba, da sauki ne lamuran da suka faru ba zato ba tsamani za su kawo tasiri ga haka. Kafin faruwar wannan lamarin amfani da makamai masu guba don kai hari, gwamnatin Amurka ta taba bayyana cewa, za ta daidaita manufarta kan kasar Syria, wato ba za ta dora muhimmanci wajen kawar da shugaban Syria daga mulki ba, hakan an kawar da cikas ga gudanar da hadin kai a tsakanin Amurka da Rasha da sauran kasashe wajen yaki da ta'addanci da murkushe kungiyar IS.

Amma, bayan faruwar lamarin a ranar 7 ga wata, Trump ya sanar da cewa, ra'ayinsa kan batun mulkin Syria ya sauya sosai. Mataimaki na musamman ga shugaban kasar Amurka dake kula da harkokin tsaron kasa Herbert McMaster, ya bayyana a ranar 9 ga wata cewa, kasarsa ta maida yaki da kungiyar IS da murkushe mulkin Bashar Al-assad a matsayin wani muhimmin al'amari. Wannan ya nuna cewa, masu tayar da lamarin kai hari ta hanyar amfani da makamai masu guba sun riga sun kawo tasiri ga kasar Amurka wajen tabbatar da manufarta kan batun Syria.

Bisa yanayin da ake ciki a yanzu, ko za a iya sarrafa halin Syria ko a'a, wannan zai tabbata ko za a iya hana tabarbarewar halin Gabas ta Tsakiya ko a'a. Idan halin da Syria ke ciki ya kara tsanani, to babu wanda ke iya daukar mulkin kasar, hakan za a tayar da rikice-rikice daban daban, a sakamakon haka, da kyar za a sake farfado da mulki da dokokin shari'a.

Watakila tabarbarewar halin Syria zai fi tsanani bisa na kasar Iraki bayan hambarar da mulkin Saddam Hussein a shekarar 2003. Amma, abin da ya fi tsanani shi ne, irin halin zai samar da dama ga 'yan ta'adda wajen samun bunkasuwa, hakan dai kokarin da kasashen duniya ke yi na dogon lokaci zai bi ruwa, balle ma irin halin zai karfafa matsalar jin kai, da yaduwar makaman kare dangi.

Kwanan baya, mayakan kungiyar IS dake kasashen Syria da Iraki sun sanar da kai farmaki kan majami'u biyu na kasar Masar, ko lamarin amfani da makamai masu guba a Syria, ko wannan farmakin da aka kai a Masar, dukkansu sun nuna cewa, yanzu halin da Syria ke ciki, har ma duk yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki na dab da tabarbarewa. Idan ba a iya sarrafa halin ba, watakila yankin Gabas ta Tsakiya zai kara samar da dama ga karuwar ayyukan ta'addanci na duniya, har zai iya zama ruwan dare ne. Idan kasashen duniya ba su iya daukar matakai da suka dace cikin sauri da kuma kai zuciya nesa ba, to mai yiwuwa ne za su fada cikin tarkon da mugun rukunoni suka yi, hakan ba za a iya tabbatar da zaman lafiya da jama'ar kasa da kasa ke fatan cimmawa ba. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China