in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 47 sun mutu a Masar sakamakon fashewar boma-bomai a wasu coci coci biyu
2017-04-10 13:07:50 cri

An samu fashewar boma-bomai a wasu cocin biyu a kasar Masar, lamuran da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 47. A sakamakon haka, shugaban kasar Abdul Fatah Al-Sisi ya sanar da kafa dokar ta baci a kasar har tsawon watanni uku.

An fara samun fashewar bom din ne a jiya da safe a cocin Mar Girgis da ke birnin Tanta a tsakiyar kasar ta Masar. A lokacin da pastoci da kuma mabiyan addinin kirista ke bikin Palm Sunday, daya daga cikin ranaku mafiya tsarki a adddinin Kirista.

Bisa labarin da gidan talabijin na gwamnatin kasar ta bayar, an ce, an dasa bom din da ya tashe ne a karkashin wata kujerar da ke cikin cocin. Sabo da ana ibada a lokacin, mutane da yawa sun mutu inda wasu kuma suka jikkata, kuma kawo yanzu, harin ya hallaka mutane 29 tare da ji wa wasu 71 raunuka a cocin dake Tanta. Nagat Assad, Kirista ce da ta gane wa idonta aukuwar lamarin, kuma ta ce, "Samari da yara sun fado, akwai jini a ko ina a cikin coci, akwai kuma sassan suminti ko ina sakamakon fashewar gini, ka iya tunawa da abubuwan da suka faru a lokacin. Har ma ana iya ganin jini a icen goruba da aka kayatar da coci da shi."

Har ila yau, da tsakiyar ranar jiya ne kuma, aka kara samun fashewar bom a cocin Saint Mark's da ke birnin Alexandria da ke arewacin kasar, inda mutane 18 suka hallaka.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa, kafin aukuwar lamarin, babban Paston Kiristoci Kifdawa Paparoma Tawadros II ya halarci bikin Palm Sunday da aka gudanar a cikin cocin.

Hoton bidiyo da aka dauka ya shaida cewa, bayan dan sanda ya hana wani mutum shiga cocin, nan da nan aka samu fashewar bom a mashigar. Abin farin ciki shi ne Paparoma Tawadros II ya riga ya bar cocin kafin harin.

Kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS ta sanar da daukar alhakin hare-haren biyu.

A birnin Tanta, Kifdawa Kiristoci da suka rasa 'yan uwansu sun nuna matukar bakin ciki da kuma fushi dangane da aukuwar lamarin.Wahby Lamie ya ce, "Su masu tsattsauran ra'ayi ba za su iya kawo baraka ga al'ummarmu ba, sai dai sun janyo mana wahalhalu. Muna matukar bakin ciki. Abin da ya faru a yau bai yi wa kowanenmu adalci ba"

Bayan faruwar hare-haren, shugaban kasar Abdul Fatah Al-Sisi ya kira taron majalisar tsaro cikin gaggawa, inda ya umurci rundunar dakaru da su taimaka wa 'yan sanda kiyaye tsaron muhimman hukumomi. A wannan rana da dare ne kuma, shugaban ya sanar da kafa dokar ta baci har na tsawon watanni uku a kasar. "Mun dauki jerin matakai domin tinkarar halin da ake ciki, kuma na farko shi ne kafa dokar ta baci ta tsawon watanni uku a duk fadin kasar kamar yadda tsarin mulki da dokoki suka tanada, a wani kokari na kare kasarmu."

Kifdawa Kiristoci sun mamaye kashi 1/10 bisa al'ummar kasar Masar da gaba daya ta kai miliyan 92, sai dai a cikin 'yan shekarun baya, sun sha fama da hare-haren da masu tsattsauran ra'ayin Islama suka kai musu. Ko a watan Disambar bara, an kai harin bom wani cocin da ke birnin Alkahira, lamarin da ya hallaka mutane 25 tare da jikkata wasu 49, kuma kamar yadda ta yi a wannan karo, kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin harin. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China