in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar shugaban Xi a kasar Finland da ganawarsa da Trump sun cimma buri na hadin gwiwa da samun moriya
2017-04-09 13:43:09 cri

A yayin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya karkare ziyarar aikin da ya kai kasar Finland, da kuma ganawar da ya yi da takwaransa shugaban kasar Amurka Donald Trump a Mar-a-lago dake jahar Florida daga ranakun 4 zuwa 7 ga wannan wata na Afrilu, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya tattaro wasu daga cikin alfanun ko kuma nasarori da wannan ziyara da kuma ganawar za ta haifar.

Na farko shi ne, karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Finland zuwa sabon mataki

Dangantaka tsakanin Sin da Finland wani muhimmin batu ne mai dogon tarihi, kana dangantakar dake tsakaninsu na kara samun tagomashi duba yadda ake kara samun fahimtar juna da cigaba cikin sauri saboda cigaban zamani da ma yadda mu'amala tsakanin kasa da kasa ke sauwaya daidai da cigaban zamani. Dangantaka tsakanin kasashen Sin da Finland, ta kasance tamkar abin koyi ce bisa dangantake dake wanzuwa tsakanin kasar Sin da kasashen Turai.

Wang Yi ya ce, wannan ziyara ta farko da shugaba Xi ya kai, ta bude wani sabon shafi game da huldar diplomasiyya da tabbatar da kafa kyakkyawar makoma da hadin gwiwa da dangantaka tsakanin kasashen biyu, wanda yana daya daga cikin ginshikan da suka assasa wannan ziyara domin cimma nasarori ta fuskar siyasa, da karafafa dangantaka, da hada gwiwa bisa matsayin koli.

Na biyu kuma dangane da tattaunawa game da dangantakar Sin da Amurka

Kasar Sin da Amurka, manyan kasashe ne biyu masu karfin fada a ji a duniya, kuma girman dangantakar dake tsakanin kasashen biyu wata hujja ce da su kansu kasashen suka tabbatar da haka, kamar yadda Wang ya tabbatar da hakan a lokacin da shugaba Xi ya karkare ziyarar aikinsa a ranar Asabar da ta gabata a kasar ta Amurka bayan tattaunawa da shugaba Trump.

Wang Yi ya ce manufar wannan ziyarar ba wai ta ta'allaka ne kan irin alfanun da al'ummomin kasashen biyu za su samu ba ne, har ma akwai wasu manufofi na cimma daidaito da ake fata dangantakar dake tsakanin kasahen biyu za ta samarwa kasa da kasa baki daya, musamman game da batun zaman lafiya da samun dauwamammen cigaba.

Bangarorin biyu sun amince cewa wannan ganawa tana da kyakkyawan sakamako, Wang ya kara da cewa, ganawar da shugaba Xi ya yi da Trump ta kara daga matsayin dangantaka da mu'amalar dake tsakanin shugabannin biyu.

Kana shugabannin biyu sun gabatarwa junansu wasu daga cikin manufofin harkokin gwamnatocinsu na cikin gida, da kuma ajandodinsu na huldar kasa da kasa, kuma wanann ganawa ta kara ingiza samun fahimtar juna, da yin aiki tare da juna, domin karfafa dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu.

Bugu da kari, Xi da Trump, sun nanata muhimmancin yin hadin gwiwa kan manufofin inganta mu'amala dake tsakaninsu.

Shugaba Xi ya ce, batun hadin kai shi ne kadai zabin da ya dace wajen gina dangantakar dake tsakanin kasar Sin da Amurka, ya kara da cewa kasashen biyu za su iya kasancewa manyan abokan hulda, yayin da a nasa bangaren Mista Trump ya ce, Amurka a shirye take ta yi aiki tare da kasar Sin wajen kawar da duk wasu turaku da za su iya yin illa game da huldar dake tsakanin kasashen biyu domin tabbatar da daga martabar dangantakar dake tsakaninsu zuwa matsayin koli.

Wang ya ce, shugabannin biyu sun ambato irin nasarorin da aka cimma ta fuskar alakar dake tsakanin sassan biyu, kana sun amince da kara kaimi wajen karfafa dangantakar kasashen biyu zuwa wani sabon mataki, domin samarwa al'ummomin kasashen biyu moriya, har ma da sauran al'ummomin duniya.

Wang Yi ya ce dukkanin kasashen biyu sun kaddamar da matakan da za su baiwa fifiko, game da hadin gwiwar dake tsakaninsu. Sin da Amurka sun amince cewa za su kara samar da kyakkyawan yanayin zuba jari da cinikayya, domin cimma matsaya don kara samun bunkasuwa da kuma fahimtar juna.

Shugaba Xi ya nanata aniyar gwamnatin Sin na yin hadin gwiwa da Amurka domin tabbatar da tsaro da aikin soja, zaman lafiya, bunkuwar tattalin arziki, inganta huldar diplomasiyya, da kuma ba da gagarumar gudunmowa wajen habakar tattalin arzikin duniya, da tallafawa harkokin cigaban kasa da kasa domin samar da kyakkyawan yanayi, da mokama mai kyau ga rayuwar bil adama a duniya baki daya.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China