Yayin wani taron manema labaru a jiyan, Firayministan kasar Stefan Lofven ya ce, dukkan alamu sun nuna cewa, farmakin da aka kai a kasar aiki ne na ta'addanci.
Har yanzu dai hukumomin tsaro a kasar ba su yi karin bayani kan al'amarin ba.
Cikin wata sanarwa da ya fitar ta bakin mai Magana da yawusa, Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi zargin cewa farmakin nuna karfin tuwo aka kai Stockholm, ya na mai jajantawa iyalan mutanen da suka mutu, tare da yi wa wadanda suka ji rauni fatan samun sauki cikin gaggawa.
Antonio Guterres ya ce MDD, ta na goyon bayan gwamnati da al'ummar kasar Sweden, inda ta ke fatan ganin an cafke tare da hukunta wadanda ke da hannu wajen kai farmakin.
Haka zalika, a jawabansu mabanbanta yayin taron kwamitin sulhu na MDD ya gudana a jiya, dukkan wakilan kasashe mambobin kwamitintin sun yi tir da farmakin.
Baya ga haka kuma, kafofin watsa labarun kasar Sweden sun bayar da labari a ranar 7 ga wata cewa, yanzu 'yan sandan sun riga sun kama mutane biyu da ake tuhumar su da hannu cikin lamarin. (Bilkisu)