in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Nijeriya ta ce allurar riga kafin cutar sankarau kyauta ce
2017-04-08 12:57:16 cri
Gwamnatin Nijeriya ta ce allurar rigafin cutar sankarau kyauta ce a duk fadin kasar, ta na mai kira ga al'ummar kasar da kada su biya ko sisi don karbar allurar.

Wata sanarwar da daraktan zaratarwa na hukumar kula da lafiya a matakin farko na kasar Faisal Shuaib ya fitar, ta yi kira ga al'ummar kasar su kai rahoton duk wata cibiya ko ma'aikacin lafiya da ya nemi kudi daga hannunsu kafin yi musu allurar, ga hukumar tsaro mafi kusa da su.

Faisa Shuaib ya ce wasu kungiyoyin al'umma sun kai rahoton cewa, wasu ma'aikatan lafiya na neman kudin ko na goro daga hannun jama'a kafin yi musu allurar, ya na mai cewa, kamar sauran alluran riga kafi, ita ma ta cutar sankarau kyauta ake yinta.

Ya ce domin dakile ci gaba da barkewar cutar, a yanzu haka, gwamnatin kasar ta samar da allurarn riga kafin cutar guda 500,000, inda kuma ake sa ran samun kari wasu 823,000.

A nata bangare, majalisar wakilan kasar ta yanke shawarar gudanar da bincike kan yadda gwamnati ke kokarin yaki da cutar da ta barke a baya- bayan nan a wasu sassan kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China