Shugaban kasar Nijer Mahamadou Issoufou, da jami'i mai kula da samar da kayayyakin aiki na kasar Kadi Abdoulaye da kuma jakadan kasar Sin dake jamhuriyar Nijer Zhang Lijun, sun halarci bikin.
A yayin da ya gabatar da jawabi, jakada Zhang Lijun, ya bayyana cewa, shirin gina babbar gadar ta Janar Seyni Kountche, shiri ne mafi girma daga cikin irin taimakon da kasar Sin take samarwa a jamhuriyar Nijer, kuma bisa hasashen da aka yi, gaba daya za a kashe kudin Sin RMB miliyan 557, kuma za'a kammala aikin gadar mai nisan kilomita 3.7 dake kudu maso yammacin birnin Niamey cikin watanni 36.
A nasa bangare, shugaba Issoufou ya nuna matukar godiya ga kasar Sin kan taimakon da ta samarwa kasarsa, ya kuma jaddada cewa, gina babbar gadar za ta yi matukar tallafawa al'ummomin kasar, musamman wajen inganta bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma a kasar ta Nijer daga dukkan fannoni. (Maryam)