Mr. Xin ya ce yanzu haka akwai masana'antu da yawan su ya kai 800 a fadin kasar, wadanda ke samar da hidimomi a fannin kayan laturoni, da kirar injina, da sinadarai, da kayayyakin amfani a asibitoci, wadanda tuni suka fara shirin raya wannan manufa.
Manufar wadda ke karkashin kudurin nan mai lakabin "Kirar kasar Sin nan da 2025", da aka fitar a shekarar 2015, na da nufin bunkasa matsayin ayyukan masana'antu, da nufin samar da ci gaba a wasu muhimman fannoni guda 10, ciki hadda na kirar na'urori masu sarrafa kan su. (Saminu)