in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin tarayyar Turai ta shimfida ka'idojin amincewarta da ficewar Birtaniya daga EU
2017-04-06 10:28:49 cri

Mambobin majalisar dokokin tarayyar Turai dake taro a Strasbourg na Faransa, sun kada kuri'ar amincewa da kudurin da ya bayyana sharuddan amincewa da ficewar Birtaniya daga EU.

Kuri'u 516 ne suka amince da kudurin, inda 133 suka ki, yayin da mambobi 50 suka kauracewa kada kuri'ar amincewa da kudurin mai kunshe da ka'idojin da majalisar dokokin ta shimfida kafin ta amince da yarjejeniyar ficewar Birtaniya daga kungiyar.

Cikin kudurin, majalisar ta jadadda bukatar dake akwai na kare hakkin al'umma, ta yadda za a rika yi wa al'ummomin kasashen EU dake zaune a Birtaniya da na Birtaniya dake zaune a kasashen EU adalci.

Majalisar ta kara da cewa, har zuwa lokacin da Birtaniya za ta fice a hukumance, za ta ci gaba da kasancewa mamba a kungiyar, abun da ke nufin cewa, har yanzu za ta samu damarmaki kamar saura tare kuma da kiyaye ka'idojin kungiyar, ciki har da harkokin kudi wadanda ka iya tsawaita har bayan ficewarta.

Matsayin Birtaniyar ta mamba a EU ya haramta mata shiga tattaunawar cinikayya da kuma kulla yarjejeniya tsakaninta da wata kasa ko kasashe mambobin EU. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China