in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Ghana ya yi kira da kara zuba jari a bangaren samar da kayayyakin more rayuwa
2017-04-06 10:19:39 cri

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya bayyana asusun samar da kayayyakin more rayuwa da zuba jari na kasar GIIF, mai jarin dala miliyan 250, a matsayin wani mmuhimmin abu da kasar za ta iya amfani da shi.

Nana Akufo Addo, ya bayyana haka ne lokacin da yake rantsar da mambobi 9 na kwamitin daraktocin asusun GIIF a fadarsa ta Flagstaff House dake Accra, babban birnin kasar.

Aikin asusun shi ne, samar da kudaden da zuba jari a bangarori daban-daban na ayyukan more rayuwa a kasar, da nufin samun ci gaba.

Da yake tabbatar da cewa, Ghana na fama da rashin muhimman kayayyakin more rayuwa a bangarori kamar na sufuri da lantarki da masanan'antu, Akufo Addo ya ce, zuba jari a bangaren samar da ababen more rayuwa zai ciyar da tattalin arziki gaba, tare da samar da guraben aikin yi.

Ya ce, kalubalen shi ne, samar da kudi da kwarewa, ta yadda za a sanya jari a bangarorin mallakar gwamnati da masu zaman kansu.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China