in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin St. Peterburg ya nuna cewa, Rasha tana fuskantar sabon kalubale a fannin yaki da ta'addanci
2017-04-05 11:00:16 cri

A ranar Litinin 3 ga wata, wani bam ya fashe a cikin jirgin kasa dake karkashin kasa a birnin St. Peterburg na kasar Rasha, a sanadin haka, mutane 14 suka rasa rayukansu, yayin harin da aka kai a wurin, shugaban kasar ta Rasha Putin yana gudanar da aikin diplomasiyya a birnin, yanzu babbar hukumar gabatar da kara ta kasar ta riga ta mayar da lamarin a matsayin harin ta'addanci, bisa sakamakon binciken da hukumar 'yan sandan kasar ta samu, an ce, kila ne mai kai harin yana da alaka da kungiyar masu tsattsauren ra'ayin addini, a saboda haka, ana ganin cewa, yanzu haka Rasha tana fuskantar sabon kalubalen ta'addanci tun bayan da ta dauki matakan yaki da ta'addanci a yankin Gabas ta Tsakiya.

Har kullum mazaunan birnin St. Peterburg suna zaman jituwa, amma yanzu sun gamu da matsala har suna mamaki kwarai saboda an kai hari a jirgin kasa dake karkashin kasa ba zato ba tsammani a Litinin da ta gabata. Tun bayan shekarar 2010, an taba kai hare hare sau da dama a kasar ta Rasha, misali a shekarar 2010, an taba kai hari a cikin jirgin kasa dake karkashin kasa a birnin Moscow, yayin harin, mutane 40 ne suka rasa rayukansu, a shekarar 2013 kuwa, an taba kai hari a tashar jirgin kasa ta birnin Volgograd dake kusa da yankin Caucasus, daga baya wato a cikin shekaru 3 da suka gabata, ba a sake kai harin ta'addanci mai tsanani a tashar jirgin kasa ko a cikin jirgin kasa dake karkashin kasa a kasar ta Rasha ba.

Yanzu hukumar bincike ta Rasha RIC ta riga ta bayyana harin a matsayin harin ta'addanci, amma sakataren watsa labarai na shugaban kasar Rasha Dmitri Peskov ya bayyana cewa, duk da cewa, an ga alamar ta'addanci a bayyane yayin da ake binciken harin, amma ana ci gaba da gudanar da bincike kan harin. Bisa sakamakon binciken da aka samu, an ce, bam da ya fashe a cikin jirgin kasa dake karkashin kasa yana da karfi sosai, shi ya sa kwararrun da abin ya shafa na kasar suna ganin cewa, kila ne an kai harin bisa shirin da aka tsara, ban da haka kuma, a lokacin da aka kai harin, shugaban kasar Putin yana birnin St. Peterburg, bisa wannan dalilin ne, harin ya kara jawo hankalin jama'a.

Yanzu hukumar bincike ta Rasha RIC ta bayyana Akbarzhon Dzhalilov mai shekaru 22 a matsayin wanda ya kai harin a jirgin dake karkashin kasa a birnin St. Peterburg, kana an bayyana cewa, kila ne yana da alaka da masu tsattsauren ra'ayi dake yankin Gabas ta Tsakiya.

Ra'ayin jama'a a kasar Rasha ya nuna cewa, kila ne harin yana da nasaba da kungiyar IS, kwararre kan nazarin harkokin kasa da kasa na Rasha Dmitry Suslov shi ma ya bayyana cewa, an kai harin ne bisa dalilin matakan yaki da ta'addancin da Rasha ta dauka a Syria.

Bayan da aka kammala yaki a jamhuriyar Chechnya, sai Rasha ta sha fama da hare-haren ta'addanci sau da dama, misali, a shekarar 2004, an yi garkuwa da mutane a Beslan, a shekarar 2010, an kai hari a jirgin kasa dake karkashin kasa a birnin Moscow da boma bomai, ana ganin cewa, wadanda suka kai hare hare su ne 'yan ta'adda na Chechnya. Abu mai faranta ran mutane shi ne tun daga shekarar 2013 har zuwa yanzu, kasar Rasha ba ta sake gamuwa da harin ta'addanci mai tsanani ba, hakan ya nuna mana cewa, kasar ta riga ta samu sakamako a bayyane a fannin yaki da ta'addanci a cikin gidan kasar. Amma tun daga watan Satumban shekarar 2015, Rasha ta fara daukar matakan aikin soja kan kungiyoyin ta'addanci, musamman ma kan IS dake cikin kasar Syria, a sanadin haka, sau da dama kungiyar IS ta sanar da cewa, za ta yi ramuwar gayya ga Rasha. Kwararrun da abin ya shafa suna ganin cewa, ban da IS, wasu kungiyoyin masu tsattsauren ra'ayi dake yankin Caucasus su ma suna aikata laifuffukan ta'addanci, a saboda haka, wajibi ne a dakile su, in ba haka ba, za su kawo babbar barazana ga tsaro da cikakken yanki a kasar ta Rasha.

A ko da yaushe shugaban kasar Rasha Putin yana nacewa ga manufar yaki da ta'addanci, shi ma ya samu cikakkiyar nasara a fannin. A shekarar bara, aka kafa rundunar sojojin tsaro ta musamman domin yaki da ta'addanci da kuma kiyaye tsaro a fadin kasar. Ana ganin cewa, an kai harin a St. Peterburg ne lokacin da Putin yake sauka a birnin, dalilin da ya sa haka shi ne domin tada hankalin jama'a a kasar, tare kuma da yi wa gwamnatin Rasha barazana. Idan an gaskanta cewa, harin yana da alaka da kungiyar IS, to, ba zai yiyu ba Rasha ta janye jiki daga harkokin yankin Gabas ta Tsakiya, har za ta kara daukar matakai domin yaki da ta'addanci a fadin duniya.

Kwararrun da abin ya shafa sun yi nuni da cewa, yanzu haka Rasha tana shiga tsakani a cikin harkokin yankin Gabas ta Tsakiya, shi ya sa kungiyoyin 'yan ta'addanci a fadin duniya sun riga sun kasance sabon kalubale ga kasar ta Rasha, a saboda haka ya kamata a kara kyautata tsarin yaki da ta'addanci tare kuma da kara karfafa hadin gwiwa dake tsakanin kasa da kasa, yanzu Rasha tana kokarin kara karfafa hadin gwiwa dake tsakaninta da kasashen Turkiyya da Iran da Iraki da dai sauran kasashen dake yankin Gabas ta Tsakiya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China