in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsagewar kasa ta hallaka mutane 234 a Colombia
2017-04-02 13:38:13 cri
Shugaban kasar Colombiya Juan Manuel Santosm, ya sanar a Jiya Asabar cewa, an kafa dokar ta baci a Mocoa, babban birnin Putumayo dake kudu maso yammacin kasar, bayan da aka samu ibtila'in tsagewar kasa wanda yayi sanadiyyar rayukan mutane 193.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya sa wasu koguna 3 dake yankin suka tumbatsa a jiya Asabar da sanyin safiya, kogunan dai sun hada da Mocoa, Sangoyaco da Mulatos, kamar yadda jaridar Colombian daily El Tiempo ta rawaito, kuma kafafen yada labaran kasar suka ambato cewa, ambaliyar ruwan tayi awon gaba da gidaje, gadoji da ababan hawa.

Ana saran adadin mutane da suka hallaka zai karu, kasancewa an kiyasta mutane kusan 200 ne har yanzu ba ji duriyarsu ba a yankin, wanda al'umma kimanin 43,000 ne ke rayuwa a yankin, kana rahotanni sun ce wasu mutanen 200 zuwa 400 sun samu raunuka a sakamakon ibtila'in.

A kalla birane 17 ne wannan bala'in ya shafa, kuma tuni shugaba Santos na kasar ya kai ziyara inda lamarin ya afku, sannan ya bada umarnin tura jami'an sojoji, 'yan sanda da sojin sama domin agazawa jami'an aikin ceto a yankin

Ko a watan Disambar bara ma, mutane sama 90 ne suka mutu a makwabciyar kasar Peru, bayan wani mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya, bugu da kari, yankunan suna fama da matsalolin sauyin yanayi ta El Nino wanda ke haddasa dumamar yanayi, wanda ke haddasa mummunan ambaliyar ruwa da tsagewar kasa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China