in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a ci gaba da goyon baya ga kiran shimfida zaman lafiya a yankin Larabawa
2017-03-30 13:45:20 cri
An rufe taron koli na kungiyar kawancen kasashen Larabawa wato AL karo na 28 a kasar Jordan, a daren ranar 29 ga wata, inda aka bayar da sanarwar Amman, wadda ta jaddada cewa, batun Palesdinu muhimmin batu ne a duniyar Larabawa, kana ta tabbatar da ci gaba da nuna goyon baya ga kiran shimfida zaman lafiya a yankunan Larabawa na shekarar 2002, tare da kira da a sa kaimi ga aiwatar da kudurin kwamitin sulhun MDD mai lamba 2334.

Sanarwar ta bayyana cewa, samun zaman lafiya mai dorewa a dukkan fannoni shi ne zabi mafi dacewa ga kasashen Larabawa, kuma kasashen za su ci gaba da kokarin sake gudanar da shawarwarin shimfida zaman lafiya a tsakanin Palesdinu da Isra'ila, da kawo karshen rikicin dake tsakaninsu.

Kaza lika sanarwar ta bayyana cewa, shirin kafa kasashe biyu hanya ce daya tilo, ta cimma samun tsaro da zaman lafiya tsakanin Palestinu da Isra'ila.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China