in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firayministan Birtaniya ta ce babu zancen sake shawara game da batun ficewar kasar daga Tarayyar Turai
2017-03-30 10:59:35 cri
Birtaniya ta sanar da ficewa daga Tarayyar Turai a hukumance, inda ta aike da wasika mai dauke da sa hannun firaministan kasar Theresa May ga shugabannin kungiyar EU mai mabobin 28 a jiya Laraba.

Theresa May, ta shaidawa majalisar dokokin kasar Birtaniya cewa, babu zancen sake shawara game da batun ficewa daga kungiyar.

An mika wasikar ne ga shugaban kungiyar EU Donald Tusk jiya da rana, kamar yadda sashe 50 na yarjejeniyar Kungiyar ta Lesbon ya tanada.

Wannan na zuwa ne watanni 9 bayan Birtaniyar ta kada kuri'ar raba gardama, inda kashi 51.9 suka amince da ficewar, yayin da 48.1 suka ki amincewa.

Bisa sashe na 50 na yarjejeniyar Lesbon, ana sa ran Birtaniya da EU su shafe shekaru biyu wajen cimma yarjejeniyar ficewar.

Idan har bangarorin biyu ba su tsawaita lokacin tatatunawar tasu ba, to Birtaniya za ta fice a watan Maris din 2019. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China