in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Somali ta amince da nada sabbin mambobin majalisar zartaswa
2017-03-30 10:42:45 cri
Majalisar dokokin Somalia ta amince da sunayen da Firaministan kasar Hassan Ali Khaire ya aike mata makon da ya gabata, inda ya ke neman amincewarta domin nada su ministoci.

A jiya Laraba ne Mataimakin shugaban majalisar wakilan kasar Abdiweli Ibrahim Mudey ya sanar da cewa, mambobin majalisar 224 ne suka kada kuri'ar amincewa da nadin mutanen, yayin da 15 suka ki amincewa, 2 kuma suka kauracewa kada kuri'ar.

Wannan mataki dai ya kawo karshen juyayin da masana suka ce ka iya nakasu ga sabuwar gwamnatin da aka kafa bayan nasarar da aka samu ta gudanar da zabe a watan Fabrerun da ya gabata.

Firaministan Somalia da ya godewa 'yan majalisar bisa amincewa da suka yi da sunayen ministocin, ya yi alkawarin daukar matakan gaggawa na tunkarar kalubalen da kasar ke fuskanta.

Ya ce gwamnatinsa za ta zage damtse wajen tabbatar da tsaro, magance matsalar fari da yaki da mayakan Al-Shabaab da kuma cin hanci tare da ciyar da tattalin arzikin kasar gaba.

Har ila yau, Hassan Ali Khaire ya kuma yi alkawarin jagorantar taronsa na farko a yau Alhamis, wanda zai mai da hankali ga matsalolin tsaro da halin fari da kasar ke ciki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China