in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Girke na'urorin kare kai a kananan tsibiran tekun kudancin Sin harkokin cikin gida ne, in ji ma'aikatar harkokin wajen Sin
2017-03-29 13:19:26 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying, ta bayyana cewa, batun shawarar girke wasu na'urorin kare kai a yankunan kasar Sin ko akasin haka, harkokin cikin gida ne na gwamnatin kasar, kuma iko ne na kare kai na kowace kasa bisa dokokin kasa da kasa.

Hua Chunying ta bayyana hakan ne, yayin da take amsa tambaya dangane da batun gina sabbin filayen saukar jiragen sama a wasu kananan tsibiran tekun kudancin kasar Sin. A yayin taron manema labarai da aka shirya jiya Talata, wani dan jarida ya yi tambayar cewa, bisa wani rahoton da Amurka ta fitar, an ce, sabon hoton da tauraron dan Adam ya dauka ya nuna cewa, kasar Sin ta rigaya ta kammala ayyukan gina wasu filayen saukar jiragen sama, a wasu kananan tsibiran dake tekun kudancin kasar, har ma akwai yiwuwar kasar za ta girke jiragen saman yakinta a wuraren. Ya ce ko wannan batu haka yake?

Da take karin haske kan hakan, Madam Hua ta ce tsibiran Nansha, yankuna ne na kasar Sin. Kuma burin kasar Sin na gudanar da ayyukan gine-gine a yankunanta, shi ne kyautata zaman rayuwa gami da kare sharadin aiki ga mutanen dake wuraren. Ta ce babu tantama, wannan harka ce ta cikin gidan kasar Sin.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China