A karkashin wannan muhimmin shiri, nan da shekaru biyar masu zuwa, hukumar WFP zata nuna goyon-baya ga gwamnatin kasar Sin, wajen inganta samar da abinci mai gina jiki ga daliban dake yankunan karkarar kasar, da tallafawa manoma masu fama da kangin talauci, da kara karfin farfado da yankunan dake yawan fuskantar barazanar bala'u.
Har wa yau kuma, shirin WFP zai nuna goyon-baya ga kasar Sin, da ma sauran wasu kasashen dake tasowa, don su samu damar bayyana yadda suke inganta tsaron abinci da rage talauci.
A nasa bangaren, wakilin hukumar WFP dake kasar Sin Qu Sixi ya bayyana cewa, a halin yanzu hukumar na yin kwaskwarima ga ayyukanta, a wani kokari na taimakawa kasar Sin, da sauran kasashen dake tasowa, cimma burin samun ci gaba mai dorewa a shekara ta 2030.(Murtala Zhang)