in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da taron kasa da kasa kan ci gaban Afirka karo na 2
2017-03-29 10:55:36 cri

Jiya Talata ne aka kaddamar da taron kasa da kasa, kan ci gaban kasashen nahiyar Afirka karo na 2 a Abidjan, babban birnin tattalin arzikin kasar Cote d'Ivoire, inda mahalartan taron za su tattauna kan batutuwan da suka shafi yadda za a warware matsalolin da kasashen Afirka suke fuskanta yayin da suke kokarin samun ci gaba.

Taron mai taken "tabbatar da shirin ci gaban Afirka" wanda za a shafe kwanaki uku ana yin sa, zai kuma tattauna kan batutuwan da suka shafi tafiyar da harkokin hukumomin jama'a da sauyawar tsarin tattalin arziki.

Makasudin taron shi ne, neman wata dabara da za ta ciyar da kasashen Afirka gaba cikin kankanin lokaci, ta hanyar yin nazari kan sakamakon da aka samu a fannin a fadin duniya.

A yayin bikin bude taron, shugaban bankin raya kasashen Afirka Akinwumi Adesina ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasashen Afirka a shekarar 2016 ya karu da kaso 2.2 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekarar 2015, a don haka, bankin ya yi imanin cewa, Afrika na da kyakkyawar makomar.

A nasa bangaren, shugaban Cote d'Ivoire Alassane Ouattara ya ce, kamata ya yi a dauki matakan da za su dace da hakikanin yanayin da kasashen Afirka ke ciki, kana gwamnatocin kasashen Afirka su kara mai da hankali kan aikin horas da kwararru, tare kuma da aiwatar da kwaskwarima a fannoni daban-daban.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China