in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fitar da rahoto game da aikin yaki da miyagun kwayoyi na 2016 a Sin
2017-03-28 11:14:58 cri

Jiya Litinin da safe, kwamitin yaki da miyagun kwayoyin kasar Sin ya fitar da wani rahoto game da yanayin da kasar ta Sin ke ciki wajen yaki da miyagun kwayoyi a shekarar 2016, inda aka bayyana cewa, a shekarar da ta gabata, adadin mutanen da suke shan miyagun kwayoyi a fadin kasar ya karu sannu a hankali, kana adadin laifuffukan da suke da nasaba da miyagun kwayoyin da hukumomin yaki da miyagun kwayoyin kasar suka tono ya kai dubu 140. Ana iya cewa, yanayin yaki da miyagun kwayoyin da kasar Sin ke ciki yanzu bai sauya sosai ba, amma akwai matsaloli iri iri da ake fuskanta.

Rahoton da aka fitar jiya a nan birnin Beijing ya yi nuni da cewa, a cikin shekarar 2016 da ta gabata, adadin mutanen da suke shan miyagun kwayoyi irin na heroin a nan kasar Sin bai karu bisa babban mataki ba, amma adadin mutanen da suke shan miyagun kwayoyi iri na methamphetamine wato miyagun kwayoyi masu haifar da guba ga motsuwar kwakkwarwar mutane da aka tace ya karu cikin sauri, kana an tarar da cewa, wasu sun fara shan sabbin nau'o'in miyagun kwayoyin da aka tace.

Darektan ofishin yaki da miyagun kwayoyin kasar Sin Liu Yuejin ya yi nuni da cewa, a halin da ake ciki yanzu, mutanen suna shan miyagun kwayoyi iri daban daban, misali irin na gargajiya kamar su heroin da tabar wiwi, da iri miyagun kwayoyi masu haifar da guba ga motsuwar kwakkwarwar mutane, da iri sabbin nau'o'in miyagun kwayoyin da aka tace ta hanyar zamani, hakan ya nuna cewa, tsarin shan miyagun kwayoyi na kasar Sin ya sauya, Liu Yuejin yana mai cewa, "A halin da ake ciki yanzu, gaba daya akwai mutanen da suke shan miyagun kwayoyi miliyan daya da dubu 505 a fadin kasar Sin, adadin da ya karu da kaso 6.8 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. A cikin su, adadin mutanen da suke shan miyagun kwayoyin masu haifar da guba ga motsuwar kwakkwarwar dan adam, ya kai miliyan daya da dubu 515, adadin da ya kai kaso 60.5 bisa dari dake cikin daukacin mutanen da suke shan miyagun kwayoyi a kasar ta Sin, kana adadin mutanen dake shan heroin ya kai kaso 38.1 bisa dari, ban da haka kuma, adadin mutanen da suke shan cannabis ko cocaine ya kai kaso 1.4 bisa dari. Daga sakamakon kididdigar da aka samu, an tarar da cewa, adadin mutanen da suke shan miyagun kwayoyi masu haifar da guba ga motsuwar kwakkwarwar dan adam ya karu cikin sauri, har ya kai kaso 81 bisa dari a cikin dukkan mutanen da suka fara shan miyagun kwayoyi a cikin shekarar bara."

Rahoton ya nuna cewa, adadin matasan da suke shan miyagun kwayoyi ya ragu a bara a nan kasar Sin, kana adadin mutane kasa da shekaru 35 da haihuwa da suka fara shan miyagun kwayoyi a bara ya ragu da kaso 19 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin shekarar 2015, hakan ya nuna cewa, kokarin da ake yi wajen gudanar da aikin yada manufar yaki da miyagun kwayoyi ya samu sakamako bisa mataki na farko.

Yanzu ana sayen yawancin miyagun kwayoyi ne daga yankin dake hada iyakokin kasashe uku wato Thailand da Myama da kuma Laos, shahararren wuri ne dake samar da miyagun kwayoyi, amma ana tace miyagun kwayoyi ne a nan kasar Sin, a shekarar bara, adadin miyagun kwayoyin da aka kwato daga hannun masu laifuffuka da aka tace a cikin kasar Sin ya kai kaso 70 bisa dari daga cikin daukacin miyagun kwayoyin da aka kwato daga hannun masu laifuffuka. Liu Yuejin ya fayyace cewa, yanzu wasu sabbin nau'o'in miyagun kwayoyi sun fito a kasar Sin. Yana mai cewa, "Tun daga farkon shekarar 2016, ofishin gwajin miyagun kwayoyin kasar Sin ya gano cewa, masu laifuffuka sun fara tace sabbin nau'o'in miyagun kwayoyi, har an rushe wuraren tace irin wadannan miyagun kwayoyi guda 8, an kuma samu irinsu masu nauyin sama da kilogrma 80, wasu saura kuwa nauyinsu ya kai sama da tan daya."

Rahoton ya ci gaba da cewa, laifin fataucin miyagun kwayoyi ya kara tsanani a kasar Sin a bara, a saboda haka hukumomin yaki da miyagun kwayoyi na kasar Sin sun kara daukar matakai domin dakile annobar, musamman ma a fannin yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta hanyar yanar gizo, Liu Yuejin yana mai cewa, "Yanzu laifin fataucin miyagun kwayoyi ta yanar gizo da laifin koyar da fasahar tace miyagun kwayoyi ta yanar gizo da laifin shan miyagun kwayoyi tare da mutane da dama suna kara tsanani a kai a kai, bara gaba daya adadin mutanen da suka aikata wadannan laifuffuka da aka kama ya kai dubu 18, nauyin miyagun kwayoyin da aka kwato daga wajensu ya kai tan 6.7, adadin tashoshin yanar gizo da suke da nasaba da laifuffukan wadanda aka rufe ya kai 128."

An ce, a cikin shekarar da muke ciki, hukumomin yaki da miyagun kwayoyin kasar Sin za su kara daukar matakai domin hana yaduwar annobar a kasar ta Sin.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China