Shugaban taron, kana ministan harkokin wajen Jordan, Ayman Al-Safadi ya yi jawabi, inda ya ce, batun Falasdinu batu ne mafi muhimmanci a gaban kome, haka kuma ya ce, kawo karshen mamayar yankunan Falasdinawa bisa shirin kasashen biyu, wani babban sharadi ne na wanzar da zaman lafiya da tabbatar da kwanciyar hankali a yankin.
Ayman Al-Safadi ya kuma jaddada muhimmancin daidaita batun Siriya ta hanyar shawarwari.
Dangane da sauran wasu batutuwan dake gaban kasashen Larabawa, ciki har da batun Libiya da batun yaki da ayyukan ta'addanci, Ayman ya ce, ya kamata a farfado da zaman lafiya da samun sulhu a fadin Libiya. Haka kuma ya ce, ya zama tilas a murkushe ayyukan ta'addanci, domin kare fararen hula.(Murtala Zhang)