in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cote d'Ivoire ta inganta tsaron mashigar teku domin tinkarar barazanar ta'addanci
2017-03-28 10:56:26 cri
Rahoton da Jaridar Fraternit'e-Matin ta kasar Cote d'Ivoire ya ce, gwamnatin kasar na karfafa matakan tsaro a manyan mashigar teku biyu na kasar, a wani kokarin tinkarar harin ta'addancin da ka iya kunno kai.

Daga ranar 20 ga watan Maris zuwa ranar 1 ga watan Afrilu, rundunar wanzar da zaman lafiya ta Amurka dake Afirka, ta shirya yin atisayen soja na hadin-gwiwa a yankin yammacin Afirka dake gabar teku, inda sojojin ruwan kasashe sama da 30 suka tafi ruwan tekun Cote d'Ivoire don gudanar da atisayen. A yayin atisayen sojan, hukumar tsaron Cote d'Ivoire ta samu bayanan sirri dake nuna cewa, akwai yiwuwar kai harin ta'addanci kasar.

Rahoton ya kuma ce, gwamnatin Cote d'Ivoire ta inganta matakan tsaronta a mashigar teku na Abidjan da na San Pedro, kana tana kara gudanar da bincike kan mashigar tekun gami da jiragen ruwan dake zirga-zirga a yankunan.

Hukumar tsaron Cote d'Ivoire ba ta kara ce kome ba game da wannan batu.

A nasa bangaren, ministan kula da harkokin cikin gida da tsaro na Cote d'Ivoire Hamed Bakayoko ya bayyana kwanan baya cewar, gwamnatin kasar za ta bada fifiko wajen yakar ayyukan ta'addanci.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China