in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dandalin Bo'ao ya fitar da sanarwar sa kaimin dunkulewar tattalin arzikin duniya
2017-03-27 14:01:06 cri

A jiya Lahadi, aka rufe taron shekara shekara na dandalin tattaunawar harkokin Asiya a garin Bo'ao na kasar Sin, inda aka fitar da sanarwar dake bayyana matakin da aka na tabbatar da dunkulewar tattalin arzikin duniya. Wakiliyarmu Lubabatu na tare da karin haske.

Bayan kammala taron dandalin tattaunawar harkokin Asiya a garin Bo'ao, an fitar da sanarwa game da matakin da za a dauka na tabbatar da dunkulewar tattalin arzikin duniya baki daya. Sanarwar ta bayyana yadda tattalin arzikin duniya ke fuskantar wahalhalu da kuma karuwar kalamai da ayyuka dake nuna kyamar dunkulewar bunkasar duniya da kuma goyon bayan kariyar ciniki a matsayin abubuwa dake kawo cikas ga harkokin ciniki da zuba jari a duniya, abin da kuma ke jefa damuwa a zukatan al'umma.

A cikin wannan hali kuma, kamata ya yi kasashen Asiya su tsaya ga bude kasuwanninsu da kuma hadin gwiwa da juna, don tabbatar da ci gaban tattalin arziki a shiyyar.

Yayin taron na tsawon yini biyu, mahalarta sun tattauna game da taken "fuskantar dunkulewar bunkasar duniya da makomar ciniki maras shinge". A ganin mahalarta taron da yawa, a yayin da wata kasa ke cikin takarar dunkulewar duniya, idan ba ta da karfi, lalle, za ta yi hasarar wasu guraben aikin yi.

A ganin babban ministan kasar Singapore, babu shakka dunkulewar bunkasar duniya zai kawo riba ga tattalin arziki, sai dai ya zama dole a kula da illolin da ke tattare da ita. Ya ce, "Ya kamata mu lura da illolin da ke tattare da dunkulewar bunkasar duniya, amma ba za a iya hana dunkulewar ba, saboda ba za a iya hana ci gaban fasahohi, da ci gaban yanar gizo ta intanet ba, amma ya zama dole a daidaita illolin da ke tattare da dunkulewar bunkasar duniya. Na farko, ya kamata a raya kasashen da ke fuskantar koma baya, na biyu kuma kasa da kasa su samar da guraben aikin yi ta hanyar horaswa, ta yadda wadanda suka rasa ayyukan yi za su iya sake samu."

Bankin AIIB na zuba jari ga raya manyan ababen more rayuwa a Asiya ya taka muhimmiyar rawa ta fuskar dunkulewar ci gaban duniya tun bayan kafuwarsa shekara guda da ta gabata. Shugaban bankin Jin Liqun ya ce, babu wanda bai amfana da dunkulewar bunkasar duniya ba, duk da cewa akwai bambancin yawan gajiyar da aka ci. Jin Liqun ya ce, zuba jari ga manyan ababen more rayuwa a yayin dunkulewar ci gaban duniya zai kara amfana wa al'umma, ya ce, "Ina son jaddada cewa, babu wanda bai amfana da dunkulewar tattalin arzikin duniya ba, duk da cewa akwai bambancin a gajiyar moriyar da suka ci. Ya yiwu wasu sun rasa ayyukan yi a cikin wata kasa, amma ya kamata a taimaka musu ta hanyar aiwatar da manufofi daga bangaren gwamnati, sabo da koke-koke ba za su amfana wa kowa ba. Don haka, zuba jari ga manyan ababen more rayuwa zai taimaka ga tuntubar juna a tsakanin gwamnatin kasa da kasa, ta yadda karin al'umma za su amfana. Sabili da haka, aikin da muke yi ba wai a zuba jari da gina layin dogo ko masana'antar samar da wuta a wata kasa ya tsaya ba, abin da muke fatan ganin shi ne za a daidaita dukkanin wadannan manyan ababen more rayuwa yadda ya kamata, ta yadda al'umma za su amfana a maimakon yin asara."

Yayin taron ministocin kudi da shugabannin manyan bankuna na kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 da aka gudanar a tsakiyar watan Maris a kasar Jamus, a sakamakon yadda kasar Amurka ta nuna rashin amincewa, ba a sanya "kin kariyar ciniki" cikin sanarwar taron ba karo na farko cikin shekaru sama da 10 da suka wuce. A sa'i daya kuma, shirin sanya haraji kan kayayyakin da kasar Amurka za ta iya aiwatarwa shi ma ya jawo ce-ce-ku-ce. Shirin ya bukaci a sanya haraji ga kayayyakin da ake shigar da su kasar, a daya bangaren kuma a kawar da haraji kan kayayyakin da take fitarwa.

A yayin taron dandalin Bo'ao, shugaban babban bankin kasar Sin, Mr.Zhou Xiaochuan ya ce, "Ban san kudurin da za a tsai da daga karshe ba, sai dai shirin zai iya taimakawa ga fitar da kayayyaki daga kasar Amurka, amma kuma zai kayyade kayayyakin da ke shiga kasar. A kasar Sin, mun yi shekaru da dama muna aiwatar da manufar bude kofa, don haka mun gane cewa, idan ana son a inganta fitar da kayayyaki kasashen ketare, lallai, ya kamata a ba 'yan kasuwa 'yancin zabar kayayyaki da kuma fasahohi da suke so, sabo da idan an kayyade abubuwan da ke shigowa daga ketare, lalle ba za su iya samar da kayayyaki masu saukin farashi ba, haka kuma ba za su iya zabar kayayyaki da fasahohi da kuma kwararru mafi kyau da suke bukata ba."

Mr.Zhou ya kuma ba da misali, inda ya ce, dalilin da ya sa yanzu haka kasar Sin ke yawan fitar da kayayyakin lantarki zuwa kasashen ketare shi ne, haraji kadan da kasar take sanyawa kan kayayyakin da ke shigowa, abin kuma da ya sa 'yan kasuwar kasar suke iya zabar kayayyaki da dama kuma masu inganci.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China