in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta gudanar da binciken kimiyya karo na biyu a yankin Qinghai-Tibet mai tsaunika
2017-03-27 11:16:22 cri
Gwamnatin yankin Tibet mai cin gashin kai da cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin sun cimma matsaya don gudanar da aikin binciken kimiyya a yankin Qinghai-Tibet mai tsaunuka, shekaru 40 da suka gabata ne aka gudanar da gwajin farko a yankin.

Masana kimiyyar za su fara aikin binciken ne a watan Yunin bana, domin gano irin sauye sauyen da aka samu game da yanayin albarkatun kasa da dazuka da mahallin halittu a tsaunukan dake yankin. Kuma za'a yi amfani da irin sakamakon da suka samu ne wajen taimakawa fannin kimiyya da kuma yin amfani da kimiyyar wajen samar da kariya ga muhalli, da tattalin arziki da kuma inganta rayuwar mazauna yankin na Tibet.

Sabbin fasahohin zamani da suka hada da yin amfani da jirage marasa matuka, da na'urorin tauraron dan adam, za'a yi amfani dasu wajen daukar hotunan taswirar wajen da kuma kididdige dukkan yankunan baki daya.

A shekarun 1970s ne aka gudanar da binciken farko a yankin, wanda ya shafi muhimman fannoni 50 da suka hada da fanni ma'adanai, da kiddigar muhalli, da kimiyyar tsirrai, da fanni dabbobi, da aikin gona da dai sauransu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China