Sanarwar ta nuna cewa, dunkulewar tattalin arzikin duniya bai daya zai samu ne sakamakon ci gaban kimiyya da fasaha. Wasu sabbin matsalolin da ake fuskanta a yanzu sun bullo ne ba domin dundulewar tattalin arziki ba ne, a maimakon haka domin tsarin gudanar da harkokin duniya da ake bi a yanzu haka bai dace da sauyawar tsarin tattalin arzikin duniyar ba. Saboda haka, dole ne a kyautata tsarin gudanar da harkokin duniya.
Baya ga haka, sanarwar ta nuna cewa, duk mambobin dandalin suna son karfafa hadin kai a fannin don taka rawarsu ta musamman wajen inganta dunkulewar tattalin arzikin duniya bai daya yadda ya kamata. (Bilkisu)