in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kamo 'yan kasar 2566 da suka tsere kasashen duniya saboda aikata rashawa
2017-03-26 12:21:07 cri
Kimanin Sinawa 2,566 ne da suke tsere zuwa kasashen duniya sama da 90 gwamnatin Sin ta maido su gida bayan ta kwato kudi kimanin yuan biliyan 8.6 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 125 karkashin shirin gwamnatin Sin na yaki da cin hanci da rashawa tsakanin shekarar 2014 zuwa 2016.

A wata sanarwar da ofishin kula da shirin maido da 'yan kasar da suka arce kasashen waje karkashin hukumar tsakiya mai yaki da rashawa, ta bayyana cewa daga cikin wannan adadin, mutane 1,283 ne suka yanke shawarar mika kansu ga gwamnatin kasar Sin bisa radin kansu.

Sanarwar ta kara da cewa, daga cikin adadin mutane 410 mambobi ne na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ko kuma wasu daga cikin ma'aikatan gwamnatin kasar.

A halin yanzu mutane 39 daga cikin mutane 100 da gwamnatin kasar Sin ke nemansu ruwa a jallo ne suka dawo gida cikin kasar ta Sin.

Sanarwar ta ce shirin yaki da rashawa tana taka rawa sosai wajen hana jami'an gwamnati da suka aikata rashawa tserewa zuwa kasashen waje. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China