in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin kasar Sin na kokarin inganta ababen more rayuwar jama'a a garuruwan Afirka
2017-03-23 12:31:14 cri

Wani rahoton da bankin duniya ya fitar a baya-bayan nan ya ce, yanzu birane da garuruwan kasashen Afirka na bunkasa cikin sauri. Haka kuma bunkasar birane da garuruwan Afirka na taka muhimmiyar rawa ta fuskar raya tattalin arzikin nahiyar. A 'yan shekarun nan, akwai karin kamfanonin kasar Sin wadanda suke kokarin bunkasa garuruwa da birane na kasashen Afirka, lamarin da ya samar da fasahohin zamani na kasar Sin ga dimbim kasashen na Afirka.

A Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, jirgin kasa na zamani na tafiya tsakanin manyan gine-gine, abun dake kawo sauki sosai ga zirga-zirgar mazauna birnin. Wannan layin dogon da aka shimfida cikin birnin Addis Ababa, ya kasance layin dogo mai aiki da wutar lantarki na farko da aka gina a yankin kudu da hamadar Sahara, wanda tsawonsa ya kai kilomita 34, haka kuma yana tafiya har na tsawon awa 16 a kowace rana. Wani babban kamfanin kasar Sin mai suna China Railway Group Limited,ya yi amfani da fasahohi gami da mizanin kasar Sin wajen shimfida layin dogon, wanda ya fara zirga-zirga daga watan Mayun shekara ta 2015.

Farashin tikitin jirgin na da araha sosai, shi ya sa yake samun karbuwa daga mazauna yankin. Alkaluma sun nuna cewa, a halin yanzu, a birnin Addis Ababa, akwai mutane kimanin dubu 60 wadanda ke yin tafiye-tafiye cikin jirgin kasan a kowace rana.

Birnin Abidjan na kasar Cote D'ivoire, mai mutane miliyan biyar, ya kasance birni mafi girma na biyu a yammacin Afirka. A kowace shekara, akwai dubun-dubatar mutanen da ke kaura zuwa birnin, lamarin a baya, ya sa ba a iya tabbatar da samar da isasshen ruwan sha ba a wasu sassan birnin. Amma a halin yanzu, matsalar karancin ruwan sha ta riga ta zama tarihi. Kamfanin gine-gine na kasar Sin mai suna CGC ne ya dauki nauyin gina wata tashar samar da tsaftaccen ruwan sha a birnin Abidjan, abun da ya warware matsalar karancin ruwan sha da mutane miliyan biyu ke fuskanta a kudancin birnin.

Shugaban tashar samar da ruwan sha ta Bonoua dake birnin Abidjan ya ce, girman birnin Abidjan na kara habaka cikin shekarun nan, kuma an yi hasashen cewa, adadin yawan mazauna birnin ya kai miliyan shida, abun da ya kara janyo bukatar wadataccen ruwa.

A halin yanzu, kamfanin CGC na kasar Sin na ci gaba da gina tasoshin samar da tsaftaccen ruwa, wadda za ta warware matsalar rashin ruwan sha da daukacin mazauna birnin Abidjan ke fuskanta, zuwa karshen shekarar nan. Shugaban tashar samar da ruwan sha ta Bonoua ya kara da cewa, ya gamsu sosai da yin hadin-gwiwa da kamfanin kasar Sin, kuma kamfanin Sin ya kawo musu fasahohin gine-gine na zamani.

Har ila yau, a birnin Luanda na kasar Angola, an gina wani babban rukunin gidaje na zamani a kudu maso gabashin birnin, inda ake samun tituna masu fadi, da gine-gine masu kyan-gani, tare kuma da cibiyar tsaftace ruwan datti. Kamfanin gine-gine na kasar Sin mai suna CITIC CONSTRUCTION shi ne ya dauki nauyin gina wannan rukunin gidaje mai suna Kilamba Kiaxi, wanda ya samu babban yabo daga kafofin watsa labaran na kasar.

Shugaban kasar Angola Dos Santos ya taba yaba da wannan rukunin gidaje cewa, shi ne ya kasance kamar wani babban abun misali ga rukunin gidaje na kasashen Afirka.

A cewar rahoton da bankin raya Afirka ya fitar, bunkasa birane da garuruwa shi ne makomar ci gaban Afirka. A halin yanzu, akwai birane da garuruwa a kasashen Afirka da dama dake bukatar jari da za'a zuba wajen samar da ababen more rayuwar jama'a.

Manazarta sun ce, bunkasar birane da garuruwan kasashen Afirka na samar da sabon zarafi ga kamfanonin kasashe daban-daban, haka kuma ya zama dole kasashen Afirka su maida hankali kan raya birane da garuruwansu cikin dogon lokaci, musamman a fannonin da suka shafi gine-gine, da zirga-zirga, da sarrafa bola, da tacewa gami da samar da ruwan sha, da kiwon lafiya da makamantansu, inda kuma a wadannan fannoni, kamfanonin kasar Sin za su taka muhimmiyar rawa a kasashen Afirka.

Wani kwararre daga hukumar samar da makamashi ta duniya ya yi nazari kan rawar da kamfanonin gine-gine na kasar Sin suka taka a fannin bunkasa birane da garuruwan kasashen Afirka, inda ya ce, salon raya biranen kasar Sin ya samar da wani misali mai kyau ga bunkasar birane da garuruwan kasashen Afirka, duba da kudi da fasahohin zamani da kamfanonin Sin ke da su. Wannan kwararre ya ce, kamfanonin kasar Sin na nuna himma da kwazo wajen zuba jari da inganta ababen more rayuwar al'umma a kasashen Afirka, abun da ya sa suka bayar da babbar gudummawa ga bunkasar birane da garuruwan kasashen Afirka, haka kuma suke samar da kuzari ga ci gaban tattalin arzikin nahiyar baki daya. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China