in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Guinea da Sin sun dauki matakan karfafa dangantakarsu
2017-03-23 10:09:19 cri
Shugaban kasar Guinea Alpha Conde da dan majalisar gudanarwar kasar Sin dake ziyara a kasar Yang Jiechi, sun amince da daukar kwararan matakan inganta huldar dake tsakanin kasashensu.

Yayin ganawarsu, Yang ya ce kasar Sin za ta yi iyakar kokarinta wajen ganin an samu ingantuwar dangantakar tare da tabbatar da kasashen biyu sun amfana da ita ta fannoni daban-daban.

Dan majalisar gudanarwar na kasar Sin, ya kuma taya shugaban kasar Guinea murnar zabensa da aka yi a matsayin shugaban Tarayyar Afrika karkashin tsarin karba-karba.

Yang ya ce a matsayinta na babbar aminiyar nahiyar, Kasar Sin na mara baya ga shugaba Conde wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa a matsayinsa na Shugaban Tarayyar Afrika, domin ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaba da tabbatar da hadin kan nahiyar, tare da inganta zaman lafiya da ci gaba.

A nasa bangare, Shugaba Conde ya ce Guinea na maraba da masu zuba jari daga kasar Sin, yana mai cewa, zuba jarin zai taimakawa kasar cika burinta na samun ci gaba mai dorewa tare da gaggauta ciyar da zaman takewa da tattalin arzikin kasar gaba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China