in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Mauritaniya ya jaddada mai da hankali kan yin hadin gwiwa da kasar Sin
2017-03-22 13:10:02 cri

Jiya Talata ne shugaba Mohamed Ould Abdel Aziz na kasar Mauritaniya, ya bayyana cewa, har kullum kasarsa na mayar da huldar da ke tsakaninta da kasar Sin a gaba da komai, yayin da take hulda da kasashen duniya. Kana kasar ta sa na mai da hankali matuka kan bunkasa hadin gwiwa da kasar Sin.

Yayin da yake ganawa da sabon jakadan kasar Sin da ke Mauritaniya Zhang Jianguo, shugaba Mohamed Ould Abdel Aziz ya gode wa kasar Sin, bisa goyon baya da taimakon ta a fannoni daban daban. Ya ce Mauritaniya za ta ci gaba da mara wa kasar Sin baya, a batutuwan da ke shafar babbar moriyar ta. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China