in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci duniya ta tashi tsaye domin kawar da nuna banbanci
2017-03-22 12:30:29 cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, a jiya Talata, ya bukaci kasashen duniya da su tsaya tsayin daka wajen magance yawaitar tashe tashen hankula, kuma su gina al'umma mai kice da son zaman lafiya da kaunar juna, don tabbatar da hadin kai a maimakon rarrabuwa.

Mista Guterres, ya ce a lokatan da ake fama da yawan tashin hankali da sauye sauye, ya ce abu ne mai sauki a iya bayyana cewa, al'umma masu karamin karfi sun fi fama da dundun matsaloli, kasancewa ana kaddamar da hare hare kan mutane saboda launin fatarsu, ko saboda kasarsu, ko kabila, ko kuma saboda addininsu.

Guterres ya fadi hakan ne a yayin da MDD ke tunawa da ranar yaki da kawar da wariyar launin fata ta kasa da kasa, wanda aka gudanar domin yaki da nuna kyama ga halayyar nuna wariya da keta hadin al'umma saboda nuna banbanci.

Da yake karin haske game da halin damuwa da bakin haure ke fuskanta, musamman mata da yara mata, wadanda suka fito daga kananan kabilu wadanda galibi su ne wadannan matsaloli suka fi shafa, sakatare janar na MDD ya bukaci a hada hannu don yin aiki tare da nufin kare hakkin bil adama baki daya.

Ya ce, kowane mutum akwai irin rawar da zai taka. Kana nuna banbancin launin fata yana matukar wargaza zaman lafiyar al'umma, yana kuma haifar da koma baya ga sha'anin demokaradiyya da harkokin gudanarwa na gwamnati. Yin aiki tare shi ne zai iya kawo karshen wadannan matsalolin domin ceto al'umma baki daya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China