in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aikin bunkasa garuruwa ya zama wani babban makomar bunkasa kasashen Afirka
2017-03-22 12:03:33 cri

Wani rahoto da bankin duniya ya fitar a baya-bayan nan ya ce, a yanzu garuruwan kasashen Afirka na bunkasa cikin sauri.

Aikin bunkasar garuruwa na taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka, amma kuma, ana bukatar zuba karin kudade wajen samar da kayayyakin more rayuwar al'umma.

A 'yan shekarun nan, a lokacin da hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da na Afirka ke kara karfafa, yawan kamfanonin kasar Sin da ke ayyukan bunkasa garuruwan Afirka na ta karuwa, inda kuma suke shigar da fasahohin kasar Sin cikin kasashen Afirka domin ba da gudummawarsu wajen bunkasa garuruwan kasashen nahiyar.

Saurayi Appo Larour, injiniya ne dake zaune a birnin Abidjan na kasar Kwadifwa.

Appo ya ce ya kan bar gida da misalin karfe 5 na sanyin safiyar kowace rana, kuma ya kan canja bas-bas har sau 5 ko 6 kan hanyar zuwa ofishin kamfanin da yake aiki a cikin garin Abidjan. Ya shaidawa wakilinmu cewa, yana bukatar sa'o'i biyu da kudin Sifa wajen dubu 1 dan zuwa wajen aikin.

Yanzu matsakaicin yawan albashi na ma'aikacin kamfanin kan kai kudin Sifa wajen dubu 100 a kowane wata, al'amarin dake nuna cewa, yawan kudin da suke kashewa na zuwa wurin aiki ya yi yawa.

Wannan wani batu ne dake bayyana yadda ake rashin kayayyakin more rayuwar al'umma a Afirka, a daidai lokacin da ake bunkasa garuruwan nahiyar.

Rahoton na bankin duniya ya nuna cewa, ya zuwa shekarar ta 2025, yawan mutanen da za su zauna a garuruwa zai karu da miliyan 187, kwatankwacin jimillar yawan al'ummar Najeriya.

Yanzu, yawan mutanen da suke zaune a garuruwa ya kai miliyan 472, amma ya zuwa shekara ta 2040, wannan adadi zai kai biliyan 1. Sakamakon haka, nahiyar Afirka za ta zama wani yanki da garuruwansa ya fi samun bunkasa cikin sauri a duk fadin duniya.

Mr. Makhtar Diop, mataimakin gwamnan bankin duniya wanda ke kula da harkokin Afirka ya ce, "aikin bunkasa garuruwa a Afirka zai samar da sabuwar damar sauya salon tattalin arzikin kasashen nahiyar."

Amma, a yanzu akwai wasu matsalolin da dole sai an hanzarta warware su, a lokacin da ake kokarin bunkasa garuruwan nahiyar.

Da farko dai, ba a samu daidaito tsakanin saurin bunkasar garuruwa da saurin bunkasar tattalin arziki. Alal misali, ma'aunin tattalin arziki na GDP ya nuna cewa a shekarar 1975, abun da aka samu daga masana'antu ya kai kashi 18 cikin dari a duk fadin Afirka, amma zuwa shekara ta 2015, wannan adadi ya ragu zuwa 11%.

Idan babu isassun masana'antu a garuruwan, to ba za a iya samar da isassun guraben aikin yi ga al'umm ba. Haka kuma, yawan kudin shiga da za a samu ba zai iya karuwa cikin sauri kamar yadda ake fata ba.

Yanzu, yawan mutanen da suke zaune a garuruwa ya kai wajen kashi 40 cikin dari bisa jimillar yawan mutanen dukkan kasashen Afirka, kuma matsakaicin yawan kudin shiga da ake samu a kowace shekara ya kai wajen dalar Amurka dubu 1.

Amma a lokacin da ake kokarin bunkasa garuruwa a galibin garuruwan kasashen yankin Gabas ta tsakiya, wannan adadin ya kai dalar Amurka 1800. Yayin da ya kai dalar Amurka 3600 a kasashen gabashin Asiya.

Bugu da kari, a lokacin da ake bunkasa garuruwa a kasashen Afirka, ana fama da matsalolin rashin babban shirin bunkasa wannan aiki, da kayayyakin more rayuwar al'umma. Yanzu ana bukatar kashe kudi da yawa idan ana son zama ko yin kasuwanci a birane da garuruwan Afirka sakamakon koma bayan kayayyakin more rayuwar al'umma.

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, idan an kwatanta kasashen sauran nahiyoyi, inda yawan kudin shiga da ake samu ya yi kama da kasashen Afirka, yawan kudin da mazauna biranen Afirka suke kashewa wajen sayen kayyayaki ya zarce kashi 29 cikin dari, kuma, yawan kudin da mazauna biranen Afirka suke kashewa a kan matsuguni ya zarce kashi 55 cikin dari.

Duk da cewa yawan kudin shiga da mazaunan biranen Afirka suke samu ba shi da yawa, kudin da suke kashewa yana da yawa, saboda tsadar kayayyaki a biranen.

Daraktan hukumar kula da zaman al'umma a birane da yankunan karkara da tunkara annoba na bankin duniya Ede Jorge Ijjasz-Vasquez ya bayyana cewa, kara zuba jari kan kayayyakin more rayuwar al'umma da yin gyare-gyare kan ikon mallakar filayen kasa bisa ka'idojin kasuwanci, muhimman matakai ne da ya kamata a dauka a lokacin da ake kokarin bunkasa tattalin arzikin birane da samar da guraban aikin yi da kuma kara karfin takarar biranen kasashen Afirka. Kasashen Afirka suna bukatar kara sa ido kan yadda ake amfani da filayen kasa, da samar da kayayyakin more rayuwar al'umma. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China