Gwamnatin kasar Kenya, da ofishin kula da yan gudun hijira na MDD (UNHCR) da IGAD, sun bayyana cikin wata sanarwa cewa, taron kolin na birnin Nairobi, zai nazarci dukkan batutuwan da suka shafi rikicin shiyya, da nufin lalibo bakin zaren warware matsalolin rikice rikice da 'yan gudun hijirar Somali suka jima suna fuskanta, kasancewar a halin yanzu sun yanke kudirin komawa garuruwansu na ainihi domin cigaba da sabuwar rayuwa.
Masu shirya taron sun ce, karuwar rikicin siyasa gami da tsanantar yanayin tsaro da ake samu a Somali, kana da yawaitar fargaba a yankunan dake karbar bakuncin 'yan gudun hijirar, ya tilasta nemo hanyoyi masu inganci na warware matsalolin da suka shafi 'yan gudun hijirar na Somali.
Hukumomin ba da agaji da jami'an gwamnatoci sun bayyana cewa, 'yan gudun hijirar Somali miliyan biyu ne suka kauracewa matsugunansu, kuma wannan shi ne adadin mafi muni a duniya wanda rikicin siyasa ya jefa al'ummar cikin yanayin matsin rayuwa wanda ya shiga shekaru na 30.(Ahmad Fagam)