in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gudanar da aikin neman likitoci mafiya jin kai wadanda suka yi aikin kyauta a ketare
2017-03-20 19:00:09 cri

 

A yau a nan birnin Beijing, kungiyar sada zumunta da al'ummomin duniya ta kasar Sin, da kwamitin kula da aikin kiwon lafiya da haihuwa bisa shirin kasar, da hukumar tabbatar da aikin samar da kayayyaki na rundunar sojan kasar Sin, suka shirya wani taron manema labaru cikin hadin gwiwa, inda suka shelanta cewa, a watan Aflilu mai zuwa, za a gudanar da aikin neman likitoci mafiya jin kai, wadanda suka yi aiki a ketare domin sada zumunci tsakanin al'ummomin Sinawa da na waje.

A yayin taron, mataimakin direktan hukumar kula da harkokin hadin gwiwa da kasashen duniya a fannin kiwon lafiya na kwamitin kula da aikin kiwon lafiya da haihuwa bisa shiri na kasar Sin Mr. Feng Yong ya bayyana cewa, tun daga shekarar 1963 har zuwa yanzu, kasar Sin ke tura tawagogin masu aikin jinya zuwa wasu kasashe masu tasowa. Ya ce ya zuwa yanzu, wannan mataki na daya daga cikin muhimman matakan tallafawa sauran kasashen duniya da kasar Sin ke dauka, kuma yana taka muhimmiyar rawa wajen karfafa zumunci, da kuma bunkasa hulda tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya, da kuma tabbatar da kiwon lafiyar al'ummomin kasashe, inda kasar Sin take tura tawagogin masu aikin jinya.

Bisa bayanin da Mr. Feng Yong ya gabatar, an ce, tun daga shekarar 1963 zuwa yanzu, kasar Sin ta tura wa kasashe da yankuna 66 na Asiya da Latin Amurka da Afirka, da Turai da kuma yankin Oceania, likitoci da sauran ma'aikatan lafiya kimanin dubu 24, wadanda suka bai wa marasa lafiya kimanin miliyan 270 taimakon jinya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China