Babbar tashar kaya ta tudu ta kasar Sin Alataw Pass, na sa ran samun karin motoci da ake shigar da su kasar a hade, da wajen 1, 000 a bana, wanda adadin ya dara na sauran tasoshin tudu na kasar.
Tashar da ta fara shigo da motoci a watan Satumba, ta shigar da hadaddun motoci 283, ciki har da 138 da aka shigar da su a cikin watanni biyu na farkon shekarar nan.
Motocin da suka hadar da kirar Land Rover, da Benz, da Toyota, da Lada sun fito ne daga kasashen Rasha, da Jamus, da hadaddiyar daular Larabawa.
Tashar na da kamfanonin dake shigar da motoci kasar guda 13, kuma sun fara shirin shigar da motoci da aka hada, tun a watan Satumban da ya gabata. Shirin dai, na ba da dama ga dillalai su saye motoci kai tsaye daga kasashen waje, inda masu saye kuma za su samu a kan farashi mai rahusa.
A farkon wannan wata ne jirgin kasa ya dauko da hadaddun motoci 120 daga Rasha, karon farko ke nan da aka shigar da motoci ta wannan hanya a tasoshi tudu na kasar. (Fa'iza Mustapha)