in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar AU ta taya sabon shugaban hukumar CAF murna
2017-03-17 20:59:30 cri
A madadin kungiyar hadin kan Afirka ta AU, shugaban hukumar zartaswar ta Moussa Faki Mahamat, ya taya sabon zababben shugaban hukumar kwallon kafar nahiyar Ahmad Ahmad murnar lashe zabe.

Mr. Mahamat ya kuma jinjinawa tsohon shugaban hukumar ta CAF Issa Hayatou, bisa gudummawar da ya baiwa hukumar,da ma ci gaban kwallon kafa a Afirka cikin tsawon shekaru.

Kafin zaben sa, Ahmad shi ne shugaban hukumar kwallon kafar kasar Madagascar, ya kuma kada Issa Hayatou wanda ke rike da jagorancin CAF din da kuri'u 34, yayin da Hayatou ya samu kuri'u 20, yayin zaben da aka kada a zaman hukumar ta CAF na 39, wanda ya gudana a helkwatar AU dake birnin Addis Ababan kasar Habasha.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China